"Akwai Lauje cikin Nadi," Atiku Ya Zargi Gwamnati da Siyasantar da Alkaluman NBS
- Jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana fargaba kan kutsen shafin NBS da aka yi a baya-bayan nan
- Hukumar kididdiga ta kasa ta ce wasu bata-gari sun kwace iko da shafinta na yanar gizo saboda haka ayi watsi da bayanansa
- Hukumar NBS ta fitar da sanarwar bayan wani rahoto da ta wallafa kan yawan kudin fansa da aka biya 'yan ta'adda a 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce akwai alamar tambaya a kan rahoton kutse a yanar gizon hukumar kididdiga ta kasa (NBS.)
Atiku Abubakar ya ce wannan al'amari wata alama ce da za ta iya nuna rashin gaskiya da kin son fadin abu yadda ya ke a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi mamakin yadda aka yi kutse a shafin NBS karo na farko a tarihi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya yi zargin siyasantar da NBS
Jaridar The Cable ta wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku ya nuna damuwa kan lokacin da aka ruwaito kutse a shafin hukumar NBS. Ya yi zargin akwai wata manufa a boye ganin cewa rahoton kutsen ya fito bayan alkaluma marasa dadi da hukumar ta fitar a kan biyan kudin fansa a Najeriya.
Atiku Abubakar ya shawarci Tinubu
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin tarayya a kan kare ingancin alkaluman hukumar kididdiga ta kasa. Ya ce;
“Ana fatan wannan batu ba wata dabara ce ba ta lalata sahihancin bayanai masu muhimmanci da ake amfani da su wajen bincike da ci gaba ba.”
Har yanzu NBS ba ta bayyana lokacin da za a dawo da shafinta na yanar gizo ba, abin da ya bar 'yan Najeriya cikin jiran bayani da kuma ƙara yawaitar shakku.
2027: Atiku ya yi martani ga Akume
A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki kalaman Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a kan siyasar 2027 mai zuwa.
Atiku na ganin kalaman Sanata Akume na neman ɗan Arewa ya hakura da fito wa takara ba ya kan hanya, ganin cewa Kudancin Najeriya ta fi dade wa a kujerar mulkin kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng