An Kai Hari kan Babban Layin Wuta a Arewa, Yankuna Sun Shiga Duhu

An Kai Hari kan Babban Layin Wuta a Arewa, Yankuna Sun Shiga Duhu

  • Layin wutar 330kV Shiroro – Katampe na kamfanin TCN ya samu matsala sakamakon barna da wasu bata-gari suka yi
  • Kamfanin rarraba wuta na TCN ya tura ma’aikatansa domin gyara layin da aka lalata kuma an fara aikin dawo da wutar
  • TCN ta yi kira ga jama’a su taimaka a hana barna kan kayayyakin wutar lantarki a Najeriya ta hanyar isar da sako ga hukuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa an sake samun barna a layin wutar lantarki na 330kV daga Shiroro zuwa Katampe a ranar Laraba.

Barnar ta saka yankuna a duhu, inda kamfanin ya fara aiki domin dawo da wutar da kuma tabbatar da ganin an hukunta masu laifi.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Lantarki
An kai hari kan babban layin wuta a Arewa. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya wallafa a Facebook, layin ya samu matsala da misalin karfe 11:43 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndidi Mbah ya ce sun gano matsalar ne yayin da layin ya dauke wuta kuma bayan an yi ƙoƙarin sake mayar masa da ita ya sake daukewa nan take.

An sace kayayyakin lantarki a Shiroro

TCN ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa bata-gari sun sace wani bangare na layin wutar lantarki tsakanin turakun T216 da T218.

Kamfanin TCN ya kuma bayyana cewa lamarin ya janyo katsewar wutar da ake kaiwa yankuna da dama.

Ma'aikatan TCN sun fara gyaran wutar lantarki

Kamfanin ya ce ya tura ma’aikatan gyara daga ofishinsa na Abuja domin maye gurbin sassan da aka lalata.

Ma’aikatan suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa wutar lantarki ta dawo nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

Kamfanin TCN ya nemi taimakon jama'a

Kamfanin TCN ya yi kira ga jama’a da su sanya ido kan kayayyakin wutar lantarki tare da kai rahoton ayyukan da ake zargin na masu lalata kayayyakin lantarki ne.

TCN ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da samar da wutar lantarki mai dorewa ga ‘yan Najeriya duk da kalubalen da ake fuskanta.

Za a samar da tashoshin lantarki a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta dauko shiri na musamman domin samar da tashoshin wutar lantarki a wasu jihohi.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce za a kashe makudan kudi wajen gina tashohin wutar lantarki a Sokoto, Ilorin da sauran jihohi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng