Tirkashi: Wani Ciyaman Ya Bi Sahun Gwamnoni, Ya Gabatar da Kasafin Biliyoyi a 2025
- Shugaban karamar hukuma a Enugu ya gabatar da kasafin 2025 na N5.5bn, wanda ya zarce N4.153bn da ya gabatar a 2024
- Kasafin kudin ya maida hankali kan manyan ayyuka kamar tituna, lafiya, aikin gona da ilimi, tare da shirin inganta kudin shiga
- Gwamnan jihar Enugu ya tallafa wa karamar hukumar ta shirin Smart Green Schools, inda ake zuba fiye da N1bn a kowace mazaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Shugaban karamar hukumar Isi-Uzo, da ke jihar Enugu, Hon. Obiora Obeagu, ya gabatar da kasafin shekarar 2025.
Hon Obiora Obeagu ya gabatarwa majalisar dokokin karamar hukumar Naira biliyan 5.5 a matsayin kasafin shekarar mai zuwa.
Ciyaman ya gabatar da kasafin kudin 2025
Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban na cewa kasafin da aka yi wa taken "Kasafin Tattalin Arziki da Sauyin Zaman Takewa" ya karu a kan kasafin N4.153bn na 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban karamar hukumar ya ce kasafin ya yi daidai da kokarin Gwamna Peter Mbah na bunkasa tattalin arzikin jihar daga dala biliyan 4.4 zuwa dala biliyan 30.
Hon. Obeagu ya ce kasafin zai tabbatar da shirin samar da abinci mai yawa, tsaron abinci, da ƙirƙirar damar aikin yi ga matasa.
Mai girma ciyaman ya kara da cewa karuwar kudin shiga na cikin gida na karamar hukumar zai taimaka wajen aiwatar da kasafin, inji rahoton This Day.
Manyan ayyuka sun lakume miliyoyin Naira
Manyan ayyuka a kasafin sun haɗa da gina tituna da gadoji, waɗanda aka ware musu Naira miliyan 860, don inganta harkokin sufuri da kawar da cinkoso.
An ware N285 miliyan ga bangaren mata, ruwa da gidaje, sannan lafiya an ware mata Naira miliyan 226 yayin da Wutar lantarki kuma ta samu Naira miliyan 200.
Naira miliyan 181 aka ware wa aikin gona, don ƙarfafa samar da abinci da ci gaban yankunan karkara.
Ilimi da rage talauci sun samu N203.8m
An ware Naira miliyan 180 ga sashen fasahar zamani, yayin da ilimi ya samu Naira miliyan 163.8. Gwamna Peter Mbah ya tallafa wa LGA ta hanyar shirin Smart Green Schools.
Sashen rage talauci da samar da ayyukan yi ya samu Naira miliyan 40. Sauran sassan sun haɗa da wasanni, muhalli, da gyaran zamantakewa.
Hon. Obiora ya tabbatar wa al’umma cewa kasafin zai kawo ci gaba mai dorewa tare da kyautata rayuwar al’ummar yankin.
Ciyaman zai fara biyan zawarawa alawus
A wani labarin, mun ruwaito cewa zawarawa za su fara karbar alawus na duk wata wata daga shugaban karamar hukumar Igbo-Ekiti a jihar Enugu, Eric Odo.
Hon. Eric Odo ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin saukaka rayuwar matan da suka rasa mazajensu a karamar hukumar Igbo-Ekiti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng