Hankalin Tinubu Ya Tashi da Jin Labarin Mutuwar Yara 35, Ya ba Gwamna Sabon Umarni

Hankalin Tinubu Ya Tashi da Jin Labarin Mutuwar Yara 35, Ya ba Gwamna Sabon Umarni

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga tashin hankali yayin da ya samu labarin mutuwar akalla yara 35 a wani taron wasanni a Oyo
  • Shugaba Tinubu ya umarci hukumomi da da gwamnatin Oyo da su binciki lamarin cikin gaggawa domin tabbatar da adalci
  • Tinubu ya jaddada muhimmancin tsaron yara da duba tsare-tsaren tsaro a duk lokacin da al'umma za su gudanar da taron jama'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna kaduwarsa kan abin da ya faru a taron wasannin yara a Ibadan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara 35.

Shugaban kasar ya miƙa sakon nta'aziyyarsa ga gwamnatin Oyo da al'ummar jihar, musamman iyalan da suka rasa 'ya'yansu a taron.

Tinubu ya yi magana yayin da yara 35 suka mutu a wani taron wasanni a Oyo
Oyo: Tinubu ya ba hukumomi da gwamna umarnin gudanar da bincike kan mutuwar yara 35. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya kadu da mutuwar yara a Ibadan

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Mutuwar yara 35: Ƴan sanda sun cafke tsohuwar matar wani babban sarki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wannan lokacin na juyayi, Shugaba Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan da abin ya shafa kuma yana rokon Allah ya ba su hakurin jure wannan rashi.
"Shugaban kasar ya umarci hukumomi da su gudanar da cikakken bincike game da wannan mummunan al'amari."

- A cewar sanarwar Onanuga.

Onanuna ya ce Tinubu ya jaddada muhimmancin gano abin da ya jawo har yaran suka mutu domin sanin ko an aikata laifi tare da bin kadin lamarin.

Tinubu ya ba gwamnatin Oyo sabon umarni

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci gwamnatin jihar Oyo da ta dauki matakai masu kyau don hana faruwar irin wannan abin a nan gaba.

Daga cikin matakan da Tinubu ya lissafa akwai duba tsare-tsaren tsaro na duk wani taro na jama'a da kuma tabbatar da bin dokokin tsaro yayin taron.

Hakanan, Shugaba Tinubu ya kira masu shirya taro da su mayar da hankali wajen kula da lafiyar duk masu halartar taron, musamman yara.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

Tinubu ya bayyana muhimmancin amfani da kwararrun jami'an tsaro, masu sa ido da masu tsara abubuwan da suka shafi tsaro a yayin taro.

'Yan sanda sun kama tsohuwar matar sarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda sun cafke tsohuwar matar sarkin Ife, Naomi Shikemi da wasu mutum bakwai kan mutuwar yara 35 a Oyo.

Rundunar ta cafke mutanen takwas ne yayin da take gudanar da bincike kan abin da ya jawo mutuwar yara 35 a wani taron wasanni da mutanen suka shirya a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.