Tallafin Noman Tinubu Ya Iso Arewa, An Ware Manoma 6,000 a Kano

Tallafin Noman Tinubu Ya Iso Arewa, An Ware Manoma 6,000 a Kano

  • Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta fara raba kayan aikin noma masu rahusa ga manoman alkama 6,000 a jihar Kano
  • Kayayyakin sun haɗa da taki da iri, inda gwamnati ta bayar da tallafin kashi 75% na kuɗin kayan domin samar da sauki ga jama'a
  • Manoman sun yaba da shirin tare da yin kira ga gwamnati da ta tabbatar da rarraba kayan ga sauran al'umma a cikin lokaci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin raba kayan aikin noma ga manoman alkama a Kano.

Hakan na cikin kokarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na wadata manona da kayan aiki domin habata noma da rage dogaro da kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

Tinubu
Tinubu ya fara raba tallafin noma a Kano. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rarraba kayan na ƙarƙashin shirin NAGS-AP da aka ƙirƙira domin ƙara yawan amfanin gona da samar da abinci mai yawa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayayyakin noma da aka raba a Kano

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari wanda ya samu wakilcin Isa Isyaku Hotoro, ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kashi 75% na kayayyakin a jihar Kano.

A yayin rabiyar, wakilin ministan ya bayyana cewa:

“Manomi zai biya kashi 25 cikin 100, domin karɓar buhunan taki uku da buhu ɗaya na irin alkama mai nauyin kilo 50,”

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa manoman 6,000 da ke cikin ƙananan hukumomin Bunkure, Ajingi, da Gaya ne za su samu kayayyakin.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an ware filaye masu fadin hekta 3,000 a wurare na musamman guda 12 domin yin noman a cikinsu.

Manoman Kano sun jinjinawa gwamnati

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

Manoman sun bayyana godiyarsu ga gwamnatin tarayya bisa kawo tallafin, suna mai cewa hauhawar farashin taki da iri ya sa da dama sun rage yawan gonakin da suke nomawa.

Sai dai sun roƙi gwamnati da ta tabbatar da cewa ana raba kayayyakin cikin lokaci domin ba su damar shiri tun da wuri.

Matar Tinubu ta raba tallafi a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta raba tallafin kudi a jihohin Najeriya.

Legit ta ruwaito cewa an raba tallafin Naira miliyan 100 ga dattawa da suka kai shekaru 65 ya yi sama a jihohin Gombe da Nasarawa a karkashin shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng