Wasu Tagwayen Bama Bamai Sun Tashi da Mutane, An Rasa Rai a Jihar Neja

Wasu Tagwayen Bama Bamai Sun Tashi da Mutane, An Rasa Rai a Jihar Neja

  • Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu bama-bamai suka tashi a Bassa da ke yankin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu yara ƴan gida ɗaya ne suka taka bom na farko, masu kai ɗauki suka taka na biyu da safiyar Alhamis
  • An ruwaito cewa mutum ɗayan da ya rasu yana cikin waɗanda suka yi yunkurin kai ɗauki lokacin da bom na farko ya tashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Wasu ababen fashewa da ake kyautata zaton bama-bamai ne sun tarwatse da mutane a kauyen Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Wani manomi mai suna Dauda Haruna ya mutu yayin da wasu mutum huɗu ciki har da ƴan gida ɗaya suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-baman.

Kara karanta wannan

Ana tuhumar tsohuwar matar sarki kan mutuwar yara 32 a makarantar Musulunci

Taswirar jihar Niger.
Wani abu da ake zaton bom ne ya tarwatse a jihar Neja, mutum guda ya mutu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a tsakanin kauyukan Bassa da Gwadara da safiyar yau Alhamis lokacin da wadanda abin ya shafa ke hanyar zuwa gona.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bama-bamai suka tashi a jere a Neja

Mazauna yankin sun shaida cewa bom na farko ya tashi ne a lokacin da ƴan uwna juna su uku, Mali (20), Nehemiah (14) da Jona (15) suka taho a babur suka taka shi.

Na biyu ya tarwatse ne yayin da wasu mutane suka taho a babur da nufin ceton yaran, ba zato suka taka wani bom din kuma ya tashi da su, ɗaya daga ciki ya mutu.

Mahaifin yara uku ƴan gida ɗaya, Mista Enoch ya labartawa manema labarai abin da ya faru a asibitin ƙwararru na IBB da ke Minna, inda aka kwantar da waɗanda suka ji rauni.

Manomi ya mutu a tashin bom

Enoch ya ce:

Kara karanta wannan

Akpabio: Shugaban majalisa ya gayawa Tinubu abin da za su yi wa kudirin haraji

"Mun shirya zuwa gona girbi, na ba ƴaƴana babur su yi gaba ni da matata muka taho a ƙafa, sun mana nisa amma mun ji kara mai karfi kamar tashin bindiga.
"Mun fata tunanin ko ƴan bindiga ne sai ga wani daga wajen ya faɗa mana wasu yara ne suka taka bom, daga nan na fahimci yara na ne."
Wasu mutum biyu daga Bassa da suka yi kokarin kai agaji sun sake taka wani bom ɗin, abin takaici ɗaya daga cikinsu ya rasu."

Bom ya hallaka manomi a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa wani manomi ya faɗa tarkon bom yayin da yake hanyar dawowa daga gona a jihar Neja.

Manomin dai ya rasa ransa sakamakon tashin bom ɗin da ya rutsa da shi a kauyen Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ranar Asabar da ta wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262