Tinubu Ya Samu Yabo daga Shugaban Majalisa, Ya Fadi Nasarorin da Ya Samu
- Shugaban majalisar dattawa ya nuna gamsuwarsa kan ayyukann samar da ababen more rayuwa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi
- Sanata Godswill Akpabio wanda ya yabawa shugaban ƙasan ya nuna cewa ayyukan da gwamnatinsa ke yi sun sanya Abuja ta koma kamar Landan
- Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa waɗannan ayyukan, musammaan na samar da tituna za su bunƙasa tattalin arziƙi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan nasarorin da ta samu a ɓangaren samar da ababen more rayuwa.
Sanata Godswill Akpabio ya yi iƙirarin cewa yanzu birnin tarayya Abuja, ya zama kamar birnin Landan.
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani zaman haɗin gwiwa na majalisar dokokin tarayya, inda Shugaba Tinubu ya gabatar da ƙudirin kasafin kudin shekarar 2025 na N47.9trn, cewar rahoton jaridar The Cable
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya yabawa Bola Tinubu
Godswill Akpabio ya yaba da ayyukan samar da ababen more rayuwa da gwamnatin ke yi, da suka hada da titin bakin teku da manyan tituna a Abuja, waɗanda ya ce sun inganta hanyoyin zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziki.
"Musamman ayyukan ka na samar da ababen more rayuwa sin share fagen samar da tituna masu yawa."
"Daga ciki har da titin bakin teku da hanyoyi masu muhimmanci a birnin Abuja, dubi yadda Abuja yanzu ta koma kamar birnin Landan."
"Wannan ci gaban ba wai kawai ya tsaya kan kankare da kwalta ba ne, yana nuna ginshiƙin tattalin arziƙinmu, haɗa jama'armu da kuma bunƙasa ci gaba."
- Sanata Godswill Akpabio
Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2025
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025, ga ƴan majalisar tarayya a babban birnin Abuja.
Shugaban ƙasan wanda ya gabatar da ƙudirin ƙasafin kuɗin a ranar Laraba, 18 ga watan Disamban 2024, ya bayyana muhimman ayyukan da za a yi a cikinsa.
Asali: Legit.ng