Ana Murnar An Rage Kudin Fetur, Darajar Naira Ta Sake Faduwa Kasa a Kasuwar Canji
- Rahoto daga kasuwar hada hadar kudi ya nuna cewa darajar Naira ta sake rikitowa kasa zuwa N1,670 kan kowace dalar Amurka
- A kasuwar hukuma, nan ma darajar Naira ta fadi daga N1,540 zuwa N1,545 kan kowace dalar Amurka a ranar Laraba, 18 ga wata
- Musa Lawal Funtua, a zantawarsa da Legit Hausa ya sanar da cewa ƙarancin daloli a kasuwar na ƙara haifar da faduwar Naira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Darajar Naira ta sake faduwa a ranar Laraba, inda darajarta ta kai N1,670 kan dalar Amurka a kasuwar bayan fage daga N1,665 na Talata.
A kasuwar musayar kuɗi ta hukuma, Naira ta fadi daga N1,540 zuwa N1,545 kan kowace dalar Amurka a rana guda.s
Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwanni
Rahoton Babban Bankin Najeriya ya tabbatar da cewa wannan saukar darajar ya haifar da faduwar N5 a kan kowace Naira, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton kasuwar hada hadar kudi ta FMDQ ya nuna cewa darajar Naira ta ragu zuwa N1,544.2 kan dalar Amurka, ragin Kwabo 15 daga ranar Talata.
Banbanci tsakanin farashin kasuwar bayan fage da NFEM ya ƙaru daga N120.95 zuwa N125 kan dalar Amurka a rana guda.
Me 'yan kasuwar canji ke cewa?
Musa Lawal Funtua, wani mai sana'ar canji a jihar Legas, ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa suna sayen dalar Amurka a kan N1655.
Har zuwa yau Alhamis, 19 ga watan Disamba, Musa Lawal ya ce suna sayar da dalar a kan N1660 ko N1665 ya danganta da yawan 'kayan.'
"Idan karshen shekara ta zo, mutane daga kasashen waje suna dawowa gida hutu, wannan ya na sa Naira ta farfado tun da suna shigowa ne da daloli daga waje.
"Amma karancin dala a cikin kasa na sawa darajar Naira ta karye, mu kanmu kasuwar mun fi son ace darajar Naira ta na tashi ba wai kullum tana faduwa ba.
"Yadda dan kasuwa ya je kasuwar bayan fage ya sayo dala, dole ne ya yi lissafin kudin da ya kashe har zuwan su Najeriya, ka ga dole ne kudin dala ya karu."
- A cewar Musa Lawal Funtua.
Dangote ya rage farashin litar fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar man attajirin Afrika, Aliko Dangote da ke Legas ta rage farashin litar man fetur ga dillallan man Najeriya.
Matatar Dangote ta sanar da cewa ta rage farashin litar fetur zuwa N899 domin saukakawa 'yan Najeriya a lokacin bukukuwan karshe da sabuwar shekara.
Asali: Legit.ng