Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda, Sun Tura Miyagu da Dama Barzahu
- Dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun fuskanci hari daga ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP
- Sojojin sun yi nasarar daƙile harin da ƴan ta'addan suka kai da safe a sansaninsu da ke Darak a ƙasar Kamaru
- Jami'an tsaron bayan samun nasarar daƙile harin, sun kuma kashe ƴan ta'adda 10 tare da ƙwato kayan abinci iri-iri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Kasar Kamaru - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) da ke aiki a ƙarƙashin sashe na 1 a Mora, sun yi nasarar daƙile wani harin ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP.
Ƴan ta'addan sun kai harin ne a wani sansanin sojoji da ke Darak a ƙasar Kamaru.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labaran rundunar MNJTF, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adda
Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar kawar da ƴan ta’adda 10 a safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2024.
"An fara kai harin ne da asuba, inda ƴan ta’addan suka kai farmaki daga wurare daban-daban a sansanin sojoji na Darak."
"A ƙazamin fadan da aka yi, sojoji sun yi artabu da ƴan ta’adda, inda suka yi nasarar hallaka ƴan ta’adda shida tare da tilastawa sauran guduwa ɗauke da raunuka daban-daban na harbin bindiga."
"Sai dai abin takaicin shi ne, sojoji biyar sun samu raunuka yayin arangamar kuma a halin yanzu ana duba lafiyarsu."
"A wani samame da suka kai, sojojin sun yi kwanton ƙauna ga ƴan ta'addan suka samu raunuka waɗanda suka tsere a kan hanyarsu da ke ƙauyen Mazogo, wanda ke tsakanin Zamba da Djibirilli."
"Sojojin sun hallaka ƴan ta’adda huɗu tare da ƙwato kayan abinci iri-iri daga hannunsu. Samamen ya sanya adadin ƴan ta’addan da aka kashe ya kai mutum 10."
- Laftanal Kanal Olaniyi Osoba
Ƴan ta'adda sun gwabza faɗa
A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi musayar wuta a tsakanin ƴan ta'addan Boko Haram da na ISWAP waɗanda ba sa ga maciji da juna.
Fafatawar da aka yi a yankin tafkin Chadi ta jawo an hallaka mayakan ƙungiyar Boko Haram guda 15 tare da ƙwato makamai masu yawa a hannunsu.
Asali: Legit.ng