Babban Malamin Musulunci, Jagora a Cibiyar Albani Zariya Ya Rasu
- Daya daga cikin manyan malamai a Daarul Hadith Salafiyyah Kaduna, Sheikh Abdullahi Assalafiy ya rasu
- An ruwaito cewa ya kasance mai kawaici, haquri, da yawan rubuce rubuce kuma ɗalibi ne na Sheikh Albani Zaria
- Malaman addinin Musulunci a gida da wajen Najeriya sun fara tura sakon ta'aziyya da jimamin rasuwar malamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - A yau Alhamis, 19 ga Disambar 2024 aka wayi gari da labarin rasuwar babban malami, Sheikh Abdullahi Muhammad Assalafiy.
An ruwaito cewa malamin ya rasu ne a jihar Kaduna kuma yana daya daga cikin jajirtattun malaman addinin Musulunci a jihar.
Sanarwar rasuwar malamin ta fito ne a cikin wani sako da daya daga cikin jagororin Cibiyar Abani Zariya, Dr Kabir Abubakar (Asgar) ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar jagora a Cibiyar Albani Zariya
Sheikh Abdullahi Assalafiy ya kasance ɗaya daga cikin manyan ɗaliban Cibiyar Daarul Hadith al-Salafiyyah kuma wakili a majalisar amintattu ta cibiyar.
A cewar Sheikh Kabir Abubakar, marigayin ya shahara da kawaici, haquri, da nisantar sha’anin duniya, tare da yawan rubuce-rubuce da hidima ga ilimin addini.
Malamin ya kasance ɗaya daga cikin manyan ɗaliban marigayi Sheikh Albani Zaria kuma shugaban Darul Hadith al-Salafiyyah a Unguwar Dosa, Kaduna.
An yi jana'izar dalibin Albani Zariya
Sheikh Umar Shehu Zariya ya bayyana rasuwar Sheikh Abdullahi Assalafiy a matsayin babban rashi ga al’umma.
Ya kuma bayyana cewa an yi jana'izar Sheikh Abdullahi Muhammad ne a kofar gidansa da ke Sabon Kawo da misalin karfe 1 na rana.
Malam Umar Shehu Zariya ya bukaci al'umma a kafar Facebook da su sanya Sheikh Abdullahi Muhammad Assalafy a cikin addu'o'insu.
An ba malamai mukami a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Neja, Mohammed Umaru Bago ya kaddamar da kwamitin Shura da malamai da masana za su jagoranta.
Gwamna Bago ya bayyana cewa kwamitin zai yi aiki wajen ba gwamnatin jihar shawari a kan lamuran da suka shafi addinin Musulunci da rayuwa.
Asali: Legit.ng