Rusau: Kotu Ta ba Kamfanin da Ya Shiga Yarjejeniya da Ganduje Gaskiya a Kano
- Babbar kotun jiha ta halasta yarjejeniyar da kamfanin Lamash properties ta kulla da gwamnatin Abdullahi Ganduje
- Kotu ta kuma umarci gwamnatin Kano, gwamna Abba da Atoni Janar su biya kamfanin diyyar biliyoyin Naira
- Jim kadan bayan hawan mulki gwamna Abba Kabir Yusuf ne aka fara rushe wasu gine-gine da aka ce an yi ba bisa ka'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Babbar kotu da ke zamanta a Kano Kano ta yanke hukunci a shari'ar rusau da kamfanin Lamash Properties ya shigar gabanta.
Kamfanin ya shaida wa kotu cewa babu dalilin da zai sa gwamnati ta rushe kadararsa a watan Yuni na shekarar 2023, kwanaki da fara mulkin Abba Kabir Yusuf.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotu ta ba kamfanin Lamash properties gaskiya, inda ta yanke hukunci biliyoyi ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun Kano ta yi hukunci a kan rusau
The Guardian ta wallafa cewa kotu ga umarci gwamnatin Kano da biyan diyyar N8,511,000,000 ga Lamash Properties Limited, mai mallakar gine-ginen da ta rushe.
Kotun ta ba da umarni ga wadanda ake kara, ciki har da gwamnatin Kano, gwamna Abba Kabir da Antoni Janar na jihar, su biya karin N10m a matsayin kudin shigar da kara.
Ikirarin kamfanin Lamash a kan gwamnatin Kano
A cikin karar da aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ma’aji, kamfanin Lamash ya ce ya samu mallakar filin bisa doka.
Kamfanin Lamash, ta hannun lauyansa, Nureini Jimoh, SAN, ya ce ya mallaki filin ne ta hanyar wata yarjejeniya da gwamnatin jihar a lokacin mulkin Gwamna Abdullahi Ganduje.
Za a shigar da gwamnatin Kano kara
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani dan kasuwa a Kano, Ibrahim Mukhtar ya zargi hukumar tsara birane ta jihar da rusa wurin sana'arsa na gidan abinci ba bisa ka'ida ba.
A zantawarsa da manema labarai a Kano, Ibrahim Mukhtar ya bayyana takaicin yadda hukumar KNUPDA ta dauki matakin da ya keta hakkinsa, kuma ya yi barazanar zuwa kotu.
Asali: Legit.ng