Mayakan Boko Haram da ISWAP Sun Gwabza Fada, 'Yan Ta'adda Sun Tafi Barzahu

Mayakan Boko Haram da ISWAP Sun Gwabza Fada, 'Yan Ta'adda Sun Tafi Barzahu

  • An fafata faɗa a tsakanin ƴan ta'addan ƙungiyoyin Boko da ISWAP waɗanda ke gaba da juna wanda ya jawo hallaka mayaƙa masu yawa
  • Ƴan ta'addan ISWAP waɗanda suka kai harin sun hallaka mayaƙan Boko Haram 15 tare da ƙwato makamai masu yawa a yayin arangamar
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƙungiyoyin ƴan ta'addan suna yawan fafatawa a tsakaninsu a ƙoƙarin da suke yi na ƙara faɗaɗa yankunan da suke iko da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƴan ta'addan Boko Haram da na ISWAP.

Faɗan da ya ɓarke tsakanin ƴan ta'addan masu gaba da juna ya jawo mutuwar mayaƙan Boko Haram 15, yayin da wasu ƴan ƙungiyar ISWAP guda biyar suka samu raunuka.

'Yan Boko Haram da ISWAP sun gwabza fada
Mayakan Boko Haram da ISWAP sun yi kazamin fada Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Ina jin zafi": Tinubu ya fadi abin da ya yi wa 'yan Najeriya ba da son rai ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan Boko Haram, ISWAP suka fafata

Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa arangamar ta faru ne a lokacin da ƴan ƙungiyar ISWAP suka kai hari kan mayaƙan Boko Haram da ke biyayya ga ɓangaren Bakura Buduma.

Harin wanda aka kai domin nuna ƙarfin iko, ya janyo ɗimbin asara ga ɓangaren Boko Haram, inda mayaƙan ISWAP suka ƙwace makamai masu yawa a yayin arangamar.

Wannan harin dai shi ne na baya-bayan nan a rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu, da suke ta gwabzawa kan albarkatun ƙasa da tasiri a yankin tafkin Chadi.

Majiyoyi sun bayyana cewa faɗan ya yi ƙamari ne a cikin ƴan watannin nan, yayin da ƙungiyoyin biyu ke ƙoƙarin faɗaɗa sansanonin su a yankin.

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'addan Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da matsa ƙaimi wajen fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa daga Najeriya.

Dakarun sojojin sun samu nasara kan ƴan ta'addan, inda suka lalata sansanoninsu guda 22 a jihihon Kebbi da Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng