Wike Ya Gamu da Gamonsa, Sojoji Sun Yi Rugu Rugu da Kayan Rusau a Abuja

Wike Ya Gamu da Gamonsa, Sojoji Sun Yi Rugu Rugu da Kayan Rusau a Abuja

  • Ana zargin wasu jami'an sojoji da bin umarnin shugabansu wajen watsa kayan rusau ana tsaka da kaddamar wa gininsa
  • An ruwaito jami'an sun yi dirar mikiya a lokacin da jami'an rusau ke tsaka da fara rushe ginin wani babban janar a Abuja
  • Jami'an sun yi laga-laga da direban da ke tuka babbar motar da ake amfani da ita wajen rusau da Wike ke yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Wasu da jami'ai sanye da kayan sojoji da ake zargin suna aiki bisa umarnin wani Janar na soji sun fatattaki jami’an kula da gine-gine da ke rusau a Abuja. Lamarin ya afku a ranar Laraba a Sabon Lugbe, Abuja, yayin da suke kokarin rushe wasu gine-gine da aka ce ba bisa ka’ida aka yi su ba bisa umarnin Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Kano: Gobara ta kone sashen gidan man NNPCL kurmus, an yi asara

Nyesom
An zargi sojoji da korar masu rusau a Abuja Hoto: HQ Nigerian Army/Nyesom Ezenwo Wike CON
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami’an birnin Abuja sun je yankin ne domin rushe katangar wani gini da ke fuloti mai lamba 416 wanda aka ce na wani Babban Janar ne.

Wike: Jami'an gwamnati sun gamu da sojoji

Wani jami’in da aka je rusau da shi ya bayyana cewa sun gamu da fushin wasu dakarun sojojin kasar nan a lokacin da su ke kokarin kaddamar da aikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in ya ce;

“Yayin da aikin rushe-rushen ke gudana, Babban Janar din ya samu labarin abin da ke faruwa. Sai ya tura sojoji biyu gidansa don su tabbatar da lamarin..

Sojoji sun lakadawa mutanen Wike duka

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun fusata da yadda jami'an hukumar gudanarwa Abuja ke kokarin ruguje gidan ubangidansu.

Wani jami'in da aka sakaye sunansa ya ce;

“Daya daga cikin sojojin, wanda aka bayyana sunansa kawai a matsayin Private Jamilu, ya nufi direban babbar motar rusau (katafila), ya kama bindigarsa, ya nufe shi kai tsaye, yana masa barazanar harbi idan bai sauko daga motar ba.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

“Direban ya sauko da ladabi, amma nan take sojojin biyu suka kama wuyansa da rigarsa, suka lakada masa duka kuma suka yaga rigarsa.

Ana zargin ana amfani da Wike don rusa PDP

A wani labarin, kun ji cewa jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Tonye Cole ya bayyana takaicin yadda jam'iyyarsa ta gagara daukar matakin korar Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Mista Cole ya bayyana cewa ana sane da yadda jam'iyya mai mulki ta APC ta ke amfani da Nyesom Wike wajen rusa PDP domin hana ta wani katabus ko zama barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.