Ana Tuhumar Tsohuwar Matar Sarki kan Mutuwar Yara 32 a Makarantar Musulunci

Ana Tuhumar Tsohuwar Matar Sarki kan Mutuwar Yara 32 a Makarantar Musulunci

  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta fara bincike kan hatsarin da ya yi sanadin mutuwar yara 32 yayin wani taron nishaɗi a Ibadan
  • An ce tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Shikemi ne ta shirya taron tare da hadin gwiwar wani ɗan jarida, Oriyomi Hamzat
  • Shaidun gani da ido sun ce cunkoson jama’a ne ya faru yayin da wasu mahalarta suka yi yunkurin shiga wurin taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta fara bincike kan hatsarin cunkoson jama’a da ya faru a Ibadan, wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar yara 32.

Hatsarin ya auku ne yayin wani taron nishaɗi da ake cewa tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Shikemi, da Oriyomi Hamzat suka shirya.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

Seyi Makinde
Yara 32 sun rasu a hatsarin jihar Oyo. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa taron ya gudana ne a wata babbar makarantar Musulunci ta Basorun a jihar Ibadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya haifar da hatsari a Ibadan

Rahotanni sun bayyana cewa an tsara taron ne domin yara 5,000 amma adadin mahalarta ya kai kusan 7,500.

Shaidun gani da ido sun ce cunkoson ya faru ne lokacin da tarin yara suka yi yunkurin kutsawa cikin wurin taron ta wata ƙofa.

Daily Post ta ce wani mahaifi ya bayyana cewa ya rasa ɗansa a yayin hatsarin kuma lamarin ya tayar masa da hankali sosai.

'Yan sandan Oyo sun fara bincike

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce bincike na kan gudana domin gano musabbabin hatsarin.

Adewale Osifeso ya ce bincike na kan tafiya, kuma za a sanar da jama’a halin da ake ciki da zarar an kammala.

Wasu iyaye sun yi kira ga gwamnati da ta sa hannu domin a saki gawarwakinsu daga asibitoci domin yi musu jana’iza.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

Martanin masu shirya taron

Manema labarai sun yi yunkurin tuntuɓar tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Shikemi, amma ba a samu amsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Hakazalika, an ce dan jarida Oriyomi Hamzat ya ce shi ma hadin gwiwa aka nemi ya yi ba wai shi ya shirya taron ba.

Gwamna ya yi ta'aziyya kan hatsarin Oyo

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi ta'aziyyar rasuwar yara da dama a makarantar Musulunci.

An ruwaito cewa gwamna Seyi Makinde ya umarci a tabbatar da gano yadda lamarin ya faru domin hukunta masu laifi wajen kisan yaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng