Kasafin 2025: Alkaluma Sun Fara Fitowa, Tinubu Ya Ware Sama da N15bn don Sayo motoci
- Alƙaluman kasafin kuɗin 2025 da Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a zaman haɗin guiwa na Majalisar tarayya sun fara fitowa
- Fadar shugaban ƙasa ta ware Naira biliyan 15.09 domin sayo motocin SUV, tayoyi, ƙananan motoci da gina ofisoshin hadiman Tinubu a 2025
- Haka nan Tinubu ya kuma ware sama da Naira biliyan 5 na aikin kula da fadar shugaban ƙasa a shekara mai zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta ware Naira biliyan 15.09 domin sayo tayoyin motocin da harsashi bai fasawa, motocin SUV da kananan motoci.
Haka zalika fadar shugaban za kuma ta yi amfani da waɗannan kuɗaden wajen gina ofisoshin mashawarta na musammana da manyan mataimaka na Tinubu.
Sannan kuma ta gabatar da jimillar kudi Naira biliyan N5.49 a matsayin tanadin kula da fadar shugaban kasa a shekara mai zuwa, kamar yadda Punch ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk wannan yana cikin kudirin kasafin kuɗin 2025 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a gaban Majalisar tarayya jiya Laraba.
Ofishin kula da harkokin kasafin kuɗi ne ya fitar da cikakken bayani da alƙaluman kasafin kuɗin 2025 yau Alhamis.
Tinubu ya gabatar da kasafin mai taken, "kasafin gyara ƙasa: samar da tsaro da wadata," a zaman haɗin guiwa na Majalisa ta 10, wamda zai laƙume Naira tiriliyan 49.7.
Ku saurari ƙarin bayani...
Asali: Legit.ng