Gwamna Abba Ya Yi Fallasa, Ya Bayyana Masu Daukar Nauyin Rikice Rikice a Kano

Gwamna Abba Ya Yi Fallasa, Ya Bayyana Masu Daukar Nauyin Rikice Rikice a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan sake ɓullar faɗace-faɗacen ƴan daba a birnin Kano
  • Abba Kabir Yusuf ya zargi ƴan adawa da ɗaukar nauyin rikice-rikicen domin tayar da hankula a jihar
  • Gwamna Abba ya sha alwashin ɗaukar tsauraran matakai domin shawo kan matsalar ta faɗan daba da ta addabi birnin Ƙano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin ɗaukar tsauraran matakai domin tunkarar matsalar ƴan daba a babban birnin jihar.

Gwamna Abba ya kuma zargi jam’iyyun adawa da ɗaukar nauyin tashe-tashen hankulan jama'a a jihar Kano.

Gwamna Abba ya zargi 'yan adawa a Kano
Gwamna Abba ya zargi 'yan adawa da daukar nauyin rikice-rikice a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene ke ɗaukar nauyin rikici a Kano?

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2024

A jawabinsa ga ƴan jarida bayan taron majalisar zartaswar jihar a ranar Laraba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi jam’iyyun adawa da haddasa tashe-tashen hankula a jihar.

Ya yi alƙawarin ɗaukar tsauraran matakai domi kawo ƙarshen sake ɓullar ayyukan ƴan daba.

Bugu da ƙari, Gwamna Abba ya bayyana cewa rahotannin sirri sun fallasa yadda shugabannin jam’iyyar adawa ke ɗaukar nauyin waɗannan ayyuka.

Ya yi zargin cewa wasu daga cikin ƴan adawa, waɗanda ba su jin daɗin ci gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar, suna kitsa rikice-rikice domin haifar da rashin zaman lafiya.

Wane mataki Gwamna Abba zai ɗauka?

Sai dai, Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar tunkarar matsalar da nufin maganceta.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara lamuntar duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ba.

An shirya tunkarar matsalar daba a Kano

Kara karanta wannan

"Ka watsar da su": Gwamnan PDP ya ba Shugaba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ƴan sanda da shugabannin unguwanni sun gudanar da taro kan matsalar daba a Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdulahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa a taron an cimma matsaya kan yadda za a samu zaman lafiya a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng