Bayan Korafe Korafe, an Cire Banar 'Jesus ba Allah ba ne' da Aka Liƙa a Masallaci

Bayan Korafe Korafe, an Cire Banar 'Jesus ba Allah ba ne' da Aka Liƙa a Masallaci

  • Bayan korafe-korafen al'umma kan wata bana da aka manna a babban masallacin Lekki da ke Lagos, an cire ta daga baya
  • Banar da aka liƙa a babban masallacin Lekki da ke jihar ta jawo ka-ce-na-ce daga ɓangarorin al'umma musamman Kiristoci
  • An wallafa wani faifan bidiyon wani daga cikin al'ummar Musulmi a yankin da ke tabbatar da cire banar tare da ba da hakuri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Bayan ce-ce-ku-ce daga al'umma, an cire banar da aka manna a gaban babban Masallacin Lekki a jihar Lagos.

An cire sanarwar da ke dauke da rubutun, 'Jesus ba Allah ba ne' bayan ce-ce-ku-ce da martani da aka samu a dandalin sada zumunta ta X.

An cire banar da ta jawo ka-ce-na-ce a masallacin Lekki
Bayan korafe-korafen al'umma, an cire banar 'Jesus ba Allah ba ne' a babban masallacin Lekki. Hoto: @tosinraj.
Asali: Twitter

An cire banar 'Jesus ba Allah ba ne' a masallaci

Kara karanta wannan

"Yesu ba Allah ba ne," Wata bana da aka liƙa a babban Masallaci ta tayar da ƙura

Wani mai amfani da X, Adeleke Opeyemi, ya wallafa bidiyon Tunde Alabi, daya daga cikin Musulmin Lekki, wanda ya ziyarci masallacin domin tabbatar da cire hoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Tunde Alabi ya ce bayyana yadda lika banar ta jawo magana a cikin al'umma inda ya tabbatar an cire ta.

“Sunana Tunde Alabi, ni mamba ne na al'ummar Musulmin Lekki, na lura da wata sanarwa da aka manna a gaban masallacinmu."
"Na lura ta janyo ce-ce-ku-ce, na aika da sako ga al'ummar masallacin kuma aka tabbatar min cewa an cire ta."
"Na zo nan domin in tabbatar da kaina, kamar yadda kuke gani, wacce aka cire tana a bayana.”

- Tunde Alabi

Wani Musulmi a Lekki ya ba da hakuri

Alabi ya nemi afuwar mutane kan abin da hakan ya haifar inda ya ce yana magana ne a karan kansa ba a madadin masallacin ba.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

Ya ce hakan ya jawo ka-ce-na-ce daga ɓangarorin al'umma musamman Kiristoci inda ya ce ya tabbatar da cire banar.

Banar 'Jesus ba Allah ba ne' ta rikita internet

Kun ji cewa wata bana da babban Masallacin Lekki a jihar Lagos ta lika ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ɓangarorin kasar.

A jikin banar an gano wani rubutu na cewa 'Jesus ba Allah ba ne' wanda mutane da dama suka yi ta martani kan banar da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.