Karyar Ƴan Bindiga da Sauran Miyagu Ta Kare a Najeriya, Sanata Ya Hango Shirin Tinubu
- Sanata Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa duba da maƙudan kudin da aka warewa tsaro a kasafin kudi, ƴan ta'adda sun shiga uku a 2025
- Ɗan majalisar dattawa ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shirya amfani da fasahar zamani ta AI domin murƙushe miyagu
- A cewarsa da zaran an samu tsaro a Najeriya, yawan ɗanyen man da ake haƙowa zai karu kuma kuɗaɗen shiga za su karu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sanatan Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, a ranar Laraba ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar tsaro.
Ibrahim, shugaban kwamitin kula da harkokin majalisa, ya ce gwamnati za ta yi amfani da fasahar AI wajen magance matsalar tsaro a shekarar 2025.
Sanata Jimoh Ibrahim ya faɗi haka ne da yake tsokaci kan warewa ɓangaren tsaro Naira tiriliyan 4.91 a kasafin kudin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga da miyagu sun shiga uku
Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv, ya bayyana cewa shekara mai zuwa za ta zama mai ɗaci ga duk wasu miyagu da ƴan tada ƙayar baya.
Ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shirya kirƙiro manhajojin da za su gano mafakar ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da ƴan ta'adda a faɗin kasar nan.
"(Tinubu) zai ba jami'an tsaro damar amfani da fasahar AI domin hana miyagu sakat a ƙasar nan.
"Idan aka cimma wannna nasara da kimanin Naira tiriliyan 5, zamu samu ƙarin kuɗin shiga kuma yawan man da ake haƙowa a rana zai ƙaru, za a samu kuɗi.
Tsaro ya inganta a Najeriya
A cewar dan majalisar dattawan, jami’an tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen ganin cewa babu wani gari ko kauye da ke karkashin ‘yan ta’addan Boko Haram.
Sanata Jimoh Ibramin ya yi ikirarin cewa alkaluma sun nuna an samu ci gaba a harkar tsaron kasar nan a gwamnatin Tinubu.
Bola Tinubu ya ba mutane dariya a majalisa
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi subutar baki inda ya kira ƴan Majalisar Tarayya ta 10 a matsayin ƴan Majalisa ta 11 yayin gabatar da kasafi.
Shugaban ƙasar ya yi koƙarin gyara wannan kuskure da ya yi amma duk da haka ya bai wa galibin waɗanda je wurin dariya.
Asali: Legit.ng