Gwamnatin Tinubu za Ta Kafa Banki na Musamman domin ba Matasa Jari
- Ministan Matasan Najeriya, Ayodele Olawande ya ce za a kafa wani banki na matasa domin bunkasa rayuwarsu
- Ayodele Olawande ya bayyana cewa Najeriya tana da sama da kashi 60% na matasa, kuma samar musu da tallafi zai kawo ci gaba
- Ma’aikatar matasa ta ce tana tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu domin aiwatar da tsare-tsare masu amfani ga matasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan matasa, Ayodele Olawande, ya ce za a kafa wani banki na musamman da zai tallafa wa matasa wajen bunkasa rayuwarsu da samun damar cimma burinsu.
Ministan ya bayyana cewa bankin matasa zai zama wani babban mataki wajen yakar talauci da rashin tsaro, musamman ta hanyar samar da damammaki ga manyan gobe.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ayodele Olawande ya yi bayanin ne a wata hira da aka yi da shi a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimmancin bankin matasan Najeriya
Punch ta wallafa cewa Ayodele Olawande ya ce kafa bankin zai zama wata babbar hanya ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tallafawa matasa.
Ministan ya ce matasa ne tushen ci gaban kowace al'umma, kuma samar da wani tsari na musamman kamar banki zai ba su damar kawo sauyi mai amfani a Najeriya.
Ya kara da cewa, wannan tsari zai ba matasa damar samun rance da tallafi domin fara kasuwanci ko kuma inganta nasu harkokin.
Rawar matasa wajen cigaban tattali
Minista Olawande ya jaddada cewa Najeriya na da sama da kashi 60 na matasa a cikin al’ummarta, wanda ke nuni da muhimmancin samar musu da tsari mai kyau.
Olawande ya ce idan har matasa suka samu dama, to ba shakka Najeriya za ta inganta sosai wajen ci gaba da kuma zaman lafiya.
Ministan ya kara da cewa a yanzu haka an dage dokar hana matasa masu yi wa kasa hidima aiki a wurare kamar bankuna domin ba su damar samun horo yadda ya kamata.
Shirin Tinubu ga matasa a 2025
A wani rahoton, kun ji cewa tarayya ta sanar da tsare tsaren da ta yi wa matsa a shekarar 2025 mai zuwa domin bunkasa rayuwarsu.
An ruwaito cewa Ministan Matasa, Ayodele Olawande ne ya bayyana tsare tsaren yayin wani shiri na musamman a jihar Borno.
Asali: Legit.ng