Kwana 1 ga Barazanar Turji, an Yi Kazamar Fada Tsakanin Yan Bindiga, an Rasa Rayuka

Kwana 1 ga Barazanar Turji, an Yi Kazamar Fada Tsakanin Yan Bindiga, an Rasa Rayuka

  • Mummunan fada ta barke tsakanin tsagin yan bindiga a jihar Katsina wanda ya yi ajalin shugabanni uku
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an gwabza ne a jiya Talata 17 ga watan Disambar 2024 a karamar hukumar Safana
  • Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Bello Turji ya rikice da aka kama amininsa, Bako Wurgi inda ya yi bazarana ga sojoji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Wani mummunan rikici tsakanin gungun 'yan bindiga ya barke a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata 17 ga watan Disambar 2024 a karamar hukumar Safana ta jihar.

An gwabza tsakanin yan bindiga a Katsina
Shugabannin yan bindiga da dama sun mutu da aka yi gumurzu a tsakaninsu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Shugabannin yan bindiga sun rasa ransu

Rahoton Zagazola Makama ya ce ƙaramin artabun ya yi sanadin mutuwar manyan shugabannin yan bindiga tare da haifar da tsoro a yankin.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya yi barazana da aka cafke babban abokinsa, ya gindaya sharadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi fada ne tsakanin gungun Yan Kambari da mabiya tsohon shugaban 'yan bindiga mai suna Usman Modi Modi.

Hakan ya janyo asarar rayuka masu yawa tare da kwace dabbobin Harisu, wanda aka san shi da kusanci da daya daga cikin gungun.

An tabbatar cewa Yan Kambari ne suka kaddamar da harin a gidan Harisu, wanda ya jawo zazzafar fafatawa da ya yi sanadin mutuwar manyan shugabanni na 'yan bindiga ciki har da Nasiru Bosho da Bala Yatsa da Audu Mankare.

Dukan wadannan da suka mutu sun rasa rayukansu ne sakamakon harbin bindiga da suka samu yayin rikicin.

Ana fargabar rigimar za ta sake kamari

Nasiru Bosho shi ne a matsayin shugaban ayyukan 'yan bindiga a karamar hukumar Safana kuma yana jagorantar sansanin Dogon Marke.

Bosho shi ne mai kula da makaman tsohon shugaban 'yan bindiga a yankin, Usman Modi Modi.

Bala Yatsa ya shahara ne bayan kisan Usman Modi Modi, yayin da Audu Mankare ya mutu bayan harbin bindiga a kirjinsa yayin gumurzu.

Kara karanta wannan

Manyan sarakunan Arewa da suka fuskanci kalubale daga gwamnoni a 2024

Ana sa ran karin rikici zai barke, domin kowanne bangare na shirye-shiryen kai farmakin ramuwar gayya.

Bello Turji ya rikice da aka cafke amininsa

Mun ba ku labarin cewa, rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya shiga wani yanayi bayan cafke amininsa, Bako Wurgi.

An tabbatar da cewa Turji ya yi gargadi ga sojoji kan sakin Wurgi ko kuma ya dauki mummunan mataki kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.