Wike: Tsohon Shugaban PDP Ya Yi Wa Ministan Tinubu Tonon Silili
- Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya taso ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a gaba
- Secondus ya tunatar da ministan na Abuja cewa da shi da sauran ƴan siyasa a jihar Rivers ne suka kai shi matsayin da ya taka
- Tsohon shugaban na PDP ya caccaki Nyesom Wike kan yadda yake ɗaukar kansa a matsayin ya fi kowa a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya caccaki ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Prince Uche Secondus ya caccaki Wike ne kan rikicin siyasar da ake yi tsakaninsa da magajinsa, Gwamna Siminalayi Fubara.
Tsohon shugaban na PDP ya yi kalaman ne a ranar Talata a yayin da ya raka, Gwamna Fubara, domin ƙaddamar da titin Bori mai tsawon kilomita 14 a ƙaramar hukumar Khana ta jihar, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara da Wike, suna takun-saka kan wanda zai yi iko da tsarin siyasar jihar Rivers.
Me tsohon shugaban PDP ya ce kan Wike?
A wajen taron, Secondus ya ce Wike ya amfana da halin kirki na ƴan siyasa a jihar Rivers.
"Masu ihu a Abuja ta yaya aka samar da su? Ikon Allah ne. Wasu daga cikinmu, da shugabannin da ke zaune a nan, sun sanya hakan ya yiwu. Allah ne a farko, saboda komai sai da nufinsa."
"Zan iya tunawa a lokacin bikin yin godiyata a coci, bayan an naɗa ni shugaban PDP na ƙasa, ya faɗi hakan a fili cewa bayan Allah, da ni da sauran shugabanni suka sa ya zama abin da ya zama."
"Yau idan ya yi magana a Abuja ko a nan, kamar ya faɗo ne kawai daga sama."
- Uche Secondus
Tsohon shugaban na PDP ya kuma bayyana Fubara a matsayin mutum mai faɗa da cikawa wanda yake mutunta dattawa.
Akpabio ya faɗi dalilin ba Wike minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Godswill Akpabio, ya bayyana dalilin shugaba Bola Tinubu na sanya Nyesom Wike a cikin ministocinsa.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa Tinubu ya ba Wike minista ne saboda ayyukan da ya yi a muƙaman da ya riƙe a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng