Yadda aka Sayar da 'Jiragen Najeriya' ga Iran alhali Gwamnati ba ta Sani ba
- Hukumar NCAA za ta rubutawa hukumar jiragen saman Iran game da jirage biyu na Azman Air da aka ce an tura Iran ba tare da izini ba
- Ana zargin an kai jiragen Airbus A340-600 da Boeing 737-300 Iran ba tare da bin dokokin takunkumin da aka sanya wa kasar ba
- Wata majiya ta yi zargin cewa jiragen sun sauka a filin jirgin Tehran Mehrabad bayan kashe wasu muhimman na'urori
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Kamfanin Azman Air na iya fuskantar takunkumi sakamakon zargin safarar jiragen sama biyu zuwa kasar Iran ba tare da bin ka’idojin kasa da kasa ba.
Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayyana cewa za ta tuntubi takwararta ta Iran domin samun karin bayani kan matsayin jiragen.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana zargin cewa tun a watan Nuwamba aka kai jiragen biyu kasar Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiragen saman da aka tura Iran
A cewar Punch, jiragen da ake magana a kansu sune Airbus A340-600 mai lamba 5N-AAM da Boeing 737-300 mai lamba 5N-YSM.
Ana zargin sayar da jiragen ga kamfanin jiragen sama na Mahan Air ba tare da sanin NCAA ba, wanda hakan ya saba wa takunkumin kasa da kasa da aka sanya wa Iran.
Rahoton Middle East Forum ya ce jirgin Airbus ya bar Kano zuwa Kabul a ranar 15 ga Nuwamba, amma matukan jirgin sun kashe wasu na'urori yayin da suka shiga sararin samaniyar Iran
Martanin hukumar NCAA
Daraktan Hulɗa da Jama’a na NCAA, Michael Achimugu ya ce hukumar za ta tuntubi takwararta ta Iran domin samun bayani kan matsayin jiragen.
Michael Achimugu ya kara da cewa, wannan matakin yana da nufin tabbatar da bin doka da ka’idojin kasa da kasa.
A halin yanzu, babu wani martani daga kamfanin Azman Air ko shugaban kamfanin, Alhaji Abdulmunaf Sarina.
Za a fadada filin jirgin Muhammadu Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta fadada filin jirgin samanda aka radawa sunan Muhammadu Buhari a jihar Borno.
Ministan harkokin sufurin jiragen saman Najeriya ne ya bayyana yadda za a fadada filin jirgin a wata ziyara da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Asali: Legit.ng