An Tsaurara Tsaro Ana Jiran Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin 2025 a Majalisa

An Tsaurara Tsaro Ana Jiran Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin 2025 a Majalisa

  • A yau Larana 18 Disamba, 2024 ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025
  • Tun da sanyin safiyar ranar ne kuma aka jibge jami'an tsaro domin tabbatar da an gabatar da kasafin cikin kwanciyar hankali
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kara tsaurara matakan shiga majalisar, yayin da ake ganin daukewar kafa a majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - An kara tsaurara matakan tsaro a majalisar tarayya gabanin bayyanar shugaban kasa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin a zaman hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai a yau.

Tinubu
Ana jiran shugaba Tinubu a majalisa Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta wallafa cewa an jibge ‘yan sanda dauke da makamai a manyan kofofin shiga cikin farfajiyar majalisar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya dawo da zancen kudirin haraji, ya cigaba da lallabar jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsaurara matakan shiga majalisar tarayya

Jami’an tsaro sun kara sanya idanu a kan shiga da fice daga majalisar kasar nan yayin da ake jiran shugaban Bola Ahmed Tinubu ya karasa.

An ruwaito cewa sai masu sahihan takardun shaidar izini ne aka bari su shiga, sannan an gudanar da tsarin tantancewa cikin sauki ba tare da wani tashin hankali ba.

An samu raguwar hayaniyar jama'a a farfajiyar majalisar da ta saba samun shige da ficen jama'a a kullum, yayin da jami'an tsaro ke kara sa ido.

Ana sa ran Bola Tinubu zai isa majalisa

Ana sa ran Shugaban kasa zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 wanda ya kai Naira tiriliyan 47.96 ga majalisar tarayya.

Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa tsarin kasafin kudin 2025 ya dogara ne a kan hasashen farashin danyen mai na $75 kowace ganga.

Kara karanta wannan

An samu matsala, Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin kudin 2025

Majalisa za ta binciki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fusata da yadda ake zargin karkatar da N111.8bn da aka ware domin shigo da kayan amfanin gona kasar nan.

Hon. Saba Ahmed, ya bukaci gano inda aka kai N111.8bn da aka ware bayan shiga yarjejeniya da kamfanin John Deere Tractors, wanda hakan ya jawo manoma su ka rasa damammaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.