Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin da 'Yan Najeriya Za Su Fara Ganin Saukin Rayuwa

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin da 'Yan Najeriya Za Su Fara Ganin Saukin Rayuwa

  • Gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan kasar nan albishir da cewa sun kusa fara jin dadin manufofin da aka zo da su
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a taron da ya gudana a ranar Talata
  • Ya ce a haka ma, manufofin gwamnati sun fara haifar da ci gaban da aka sa rai za su samar domin bunkasar tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fito da bayanai a kan lokacin da mazauna kasar nan za su fara samun saukin matsin rayuwa da su ke ciki.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayar da tabbacin shekarar da ‘yan Najeriya za su fara sharbar ribar manufofin gwamnati.

Kara karanta wannan

An samu matsala, Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin kudin 2025

Tinubu
Gwamnati ta ce manufofinta sun fara haifar da da mai ido Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Twitter

TVC news ta wallafa cewa Mohammed Idris ya bayyana haka ne a wani taro bita da aka gudanar da Voice of Nigeria a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta fadi shekarar bunkasar arziki

Jaridar Businessday ta ruwaito cewa Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ya ce tuni tsare-tsaren gwamnati su ka fara haifar da da mai ido.

Ya kara da nanata cewa daga shekarar 2025 da za ta kama a cikin ‘yan kwanaki ne ‘yan Najeriya za su fara ganin ribar manufofin da gwamnatinsu ta zo da su.

“A yada ayyukanmu,” inji Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bukaci kafafen yada labarai da su tabbata an yada ci gaban da manufofinta za su samar idan lokacin ya yi.

Mohammed Idris ya yi kira na musamman ga VON, a matsayin kafar yada labarai ta kasa, ya kamata ta fito da yadda Najeriya ta kama sabon tafarki na farfadowar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn

Majalisa za ta binciki gwamnatin Tinubu

A baya mun ruwaito cewa majalisar wakilan kasar nan ta shirya binciken yadda aka kashe wasu makudan kudi wajen inganta harkokin noma wanda kudinsa ya kai N111.8bn.

Majalisar za ta binciki dalilin rashin kawo sama da manyan taraktoci 2,000 da injinan noma 100 bayan an shiga yarjejeniya da kamfanin John Deere Tractors domin shigo da kayan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.