Tsohon Sufeta Janar Ya Fadi 'Dan Siyasa 1 daga Arewa da Zai Iya Hada kan Najeriya
- Solomon Arase ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin ginshiki na haɗin kai wanda ya yaki cin hanci, ya inganta tsaro da cigaba
- Tsohon Sufeta Janar din ya gode wa Buhari kan damar da ya ba shi na shugabantar hukumar kula da ‘yan sandan Najeriya
- Solomon ya ce tsohon sojan ya yi shugabanci mai cike da sadaukarwa, tawali’u da jajircewa wanda ke tasiri ga hadin kan kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon Sufeta Janar na ‘yan sanda, Solomon Arase, ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin ginshikin haɗin kan Najeriya ko bayan barinsa ofis.
A cikin yabo na musamman don taya Buhari murnar cika shekaru 82, Arase ya ce Buhari ya kafa tarihi da dasa wani sabon tunanin hadin kai a Najeriya.
Arase ya ce Buhari ya yaki cin hanci, ya inganta tsaro da samar da cigaban kayan more rayuwa da za su amfani Najeriya na dogon lokaci, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Muhammadu Buhari ya hada kan Najeriya' - Arase
Tsohon shugaban 'yan sandan ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai tawali’u da tsantsar hali mai kyau wanda ke ba wa mutane kwarin guiwa ko bayan shugabancinsa.
Ya kuma gode wa Shugaba Buhari kan damar da ya ba shi na shugabantar hukumar kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya.
Arase ya ce rayuwar Buhari tana cike da sadaukarwa, tsayayyen tunani da kuma son ci gaban ƙasa musamman ta fuskar haɗin kan Najeriya.
'Buhari ya yi shugabanci na gaskiya - Arase
Ya tunatar da irin jarumtar Buhari tun daga matsayinsa na matashin soji har zuwa shugabancin mulkin soja da na dimokuraɗiyya.
Arase ya ce mulkin Buhari, wanda aka gina shi a kan gaskiya, rikon amana da jajircewa, ya yi tasiri mai yawa ga rayuwar ‘yan Najeriya.
Tsohon sufetan ya yi fatan Allah ya ci gaba da ba wa Buhari lafiya, kwanciyar hankali da nisan kwana yayin da yake murnar cika shekaru 82.
Dangote ya ziyarci Buhari a garin Daura
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya sun yi martani mai zafi yayin da Aliko Dangote ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa na Daura, jihar Katsina.
Dangote bisa rakiyar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun ziyarci Buhari domin taya shi murnar cika shekaru 82, lamarin da ya jawo ka-ce-na-ce.
Asali: Legit.ng