Dangote Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, An Gano Dalili a cikin Bidiyo
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 82 a ranar 17 ga Disamba, inda ya karɓi baƙi a gidansa na Daura
- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote da tsohon Sakataren gwamnati, Boss Mustapha, sun ziyarci Buhari
- Wasu ‘yan Najeriya sun yi martani a kan bidiyon Dangote da Boss Mustapha yayin da suka ziyarci Buhari don taya shi murna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a Daura, jihar Katsina.
Aliko Dangote ya samu rakiyar tsohon sakataren gwamnati, Boss Mustapha, yayin wannan ziyarar ta taya Buhari murnar cika shekaru 82 da haihuwa.

Asali: Twitter
Dangote ya ziyarci Muhammadu Buhari a Daura
Bashir Ahmad, tsohon mataimaki na musamman kan harkokin sadarwar zamani ga Buhari, ya wallafa bidiyon Dangote da Mustapha a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Tsohon Sufeta Janar ya fadi 'dan siyasa 1 daga Arewa da zai iya hada kan Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Boss Mustapha, tsohon sakataren gwamnati da shugaban Dangote Group sun kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a ranar cikarsa shekaru 82 da haihuwa."
- A cewar Bashir Ahmed.
‘Yan Najeriya sun yi martani kan ziyarar Dangote
@FOdorige
"Wadanda suka ci gajiyar gwamnatinsa ke zuwa.
"Ya kamata Godwin Emefiele ma ya kai masa ziyara."
@AbdulqudusO_
"Duk wadanda suka ci gajiyarsa za su kawo ziyara… Babu wanda ya ci gajiyar gwamnati ya ga laifin wannan gwamnatin."
@ONil9092
"Aikin tallatta mafi munin shugaban da duniya ta taɓa samu."
Tsohon gwamna ya ziyarci Buhari a Daura
A dan tsakanin ne, tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun, ya kai wa Buhari ziyara a gidansa na Daura, don taya shi murnar cika shekaru 82.
Bidiyon da ya nuna Amosun da wasu suna yi wa tsohon shugaban Kasa Buhari waka ya bazu a kafafen sada zumunta tare da janyo martani daban-daban.
Bashir Ahmad ya wallafa hotuna da bidiyon bikin a shafinsa na sada zumunta a ranar Talata, 17 ga Disamba.
Ooni na Ife ya yaba salon mulkin Buhari
A wani labarin na daban, Legit Hausa ta rahoto cewa Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya kai wa Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a garin Daura, jihar Katsina.
Oba Adeyeye, a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai ya bayyana dalilin da ya sa ya ziyarci tsohon shugaban kasar da kuma abinda suka tattauna a kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng