Duk da Rashin Tsaro, Malami na Tafiyar 25km a Keke domin Koyarwa a Katsina
- Wani malamin makaranta ya dauki hankulan al'umma a jihar Katsina ganin yadda yake sadaukar da rayuwarsa a aikinsa
- Malamin mai Nura Ibrahim ya fadi yadda yake tafiyar kilomita 25 daga Funtua zuwa makarantar da ke Tumburkai
- Malamin yayin zantawa da wakilin Legit Hausa ya ce ya sadaukar da rayuwarsa duk da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Mutane da dama sun yi ta yada labarin wani malamin makaranta a jihar Katsina da yake sadaukar da rayuwarsa.
Malamin mai suna Nura Ibrahim yana tafiyar fiye da kilomita 25 a kan keke kullum domin koyarwa a makaranta.
Malam Nura ya fadi yadda yake tafiyar 56km
Malamin ya bayyana haka ne yayin da wakilin Legit Hausa ya zanta da shi da yammacin yau Talata 17 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Nura ya ce yana koyarwa ne a makarantar sakandare ta GDSS Tumburkai inda yake tashi daga garin Funtua.
"Sunana Nura Ibrahim, ina koyarwa a makarantar GDSS, Tumburkai da ke karamar hukumar Dandume a jihar Katsina."
"A kalla a kowace safiya ina tafiyar ya kai kilomita 56 zuwa Tumburkai daga Funtua."
"Babban abin da ya sa na ke tafiya da keke saboda halin kunci da ake ciki, akalla zan kashe N3,000 zuwa da dawowa idan na ce zan yi amfani da abin hawa na kasuwa."
- Malam Nura Ibrahim
Yadda Malam Nura ya sadaukar da rayuwarsa
Malam Nura ya kara da cewa yana sadaukar da rasuwarsa ne duk da rashin tsaro da ake fama da shi saboda aiki ne dole sai ya je.
Malamin ya ce idan ya ce zai rika amfani da abin hawa na kasuwa albashin ba shi da wani kauri kudin abinci ma kawai ya isa.
Matsalolin da ke hana yara zuwa makaranta
A wani labarin, kun ji cewa Ilimi a Arewacin Najeriya na fuskantar barazana duba da matsalolin da ke hana yara zuwa makaranta.
Daga cikin kalubalen da suke fuskanta akwai rashin tsaro da talauci da al’adun da ke hana yara zuwa makaranta wanda ke bukatar dakilewa.
Asali: Legit.ng