'Akwai Aiki a Gabanku': Aminu Ado Bayero Ya Shawarci Malamai da Limamai kan Yan Daba
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya nuna damuwa kan yadda yan daba suka addabi al'umma
- Sarkin ya bukaci iyayen yara da hukumomi da su kara sanya ido wurin tabbatar da kula da 'ya'yansu
- Hakan ya biyo bayan yawan ayyukan ta'addanci da ya zama ruwan dare wanda ya yi ajalin rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya koka kan ayyukan yan daba a jihar.
Basaraken ya yi kira ga al'ummar jihar da su zauna lafiya da juna domin samun cigaba a Kano.
Aminu Ado ya koka kan ayyukan daba
Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Masarautar Kano ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci al'umma su cigaba da kaunar juna a tsakaninsu tare da gujewa duk wani abu da zai kai ga tayar da zaune tsaye ko fadan daba.
Sarkin ya koka kan yadda yan jihar suka tsinci kansu, musamman ma rikice-rikicen daba da suka jawo asarar rayuka a cikin birnin Kano.
"Ina kira ga limaman masallacin Juma'a da malamai da su cigaba da wa'azi da kuma fadakar da al'umma."
"Ina tunatar da hukumomi da jagororin al'umma da su kula da nauyin da Allah ya daura musu na kare da lafiya da dukiyoyi."
- Cewar sanarwar
Yan daba: Aminu Ado ya shawarci iyayen yara
A kan haka, Sarkin ya bukaci iyaye su kasance masu lura da amanar ‘ya’yan da Allah ya ba su kan nauyin da ya dora musu.
Haka zalika, Sarkin ya tunatar da gwamnatocin jihohi da jagororin al’umma su kula da nauyin da ke kansu na tabbatar da lafiya da kariya ga rayuka da dukiyoyi.
Gyaran masarauta: Kotu ta dakatar da Aminu Ado
Kun yi cewa wata babbar kotun Kano ta yi hukunci kan buƙatar gwamnatin jihar ta hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero gyara fadar Nasarawa.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Dije Abdu-Aboki ta sake hana shi gyara fadar Nasarawa da yake zaune a cikinta bayan an sauke shi.
Asali: Legit.ng