Matar Tinubu Ta Shigo Arewa Ta Raba Miliyoyin Naira a Jihohi
- Matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta bai wa mutane da dama tallafin miliyoyin Naira Nasarawa da Gombe
- Shirin raba tallafin na cikin tsare-tsaren Renewed Hope Initiative domin tallafa wa tsofaffi 'yan sama da shekaru 65 a Najeriya
- An ware Naira biliyan 1.9 domin rabawa tsofaffi a jihohin Najeriya 36 da Abuja, ciki har da samar da kula da lafiya a kyauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da rabon tallafin Naira miliyan 50 ga tsofaffi 250 daga kananan hukumomin Nasarawa da Gombe.
A Nasarawa, taron ya gudana ne a birnin Lafia a karkashin shirin Renewed Hope Initiative Elderly Support Scheme, wanda aka kaddamar domin tallafa wa tsofaffi 'yan sama da shekaru 65.

Asali: UGC
Punch ta wallafa cewa tallafin na daga cikin kokarin rage radadin kalubalen tattalin arziki da 'yan Najeriya ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin bayani kan tallafin matar Tinubu
Uwargidan Shugaban Kasa ta bayyana cewa an ware Naira biliyan 1.9 domin rabawa tsofaffi a jihohin Najeriya, ciki har da Abuja.
A wannan karon, an kara adadin kudin tallafin daga N100,000 zuwa N200,000 domin kara tallafa wa tsofaffi a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Matar shugaban kasar ta bayyana cewa tsofaffi daga kungiyar matan jami'an tsaro da sojoji za su amfana daga shirin.
Remi Tinubu za ta fara tallafin lafiya
Sanata Tinubu ta sanar da cewa za a kaddamar da shirin kula da lafiyar tsofaffi kyauta a duk fadin kasar nan domin inganta rayuwarsu.
Ta kuma jinjinawa uwargidan gwamnan Nasarawa, Salifat Abdullahi-Sule da sauran matan gwamnoni bisa jajircewarsu wajen inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan
Kama tsofaffin gwamnoni, ministoci da manyan nasarorin EFCC da ICPC a shekarar 2024
An raba tallafin matar Tinubu a Gombe
A jihar Gombe, matar shugaban kasar ta raba tallafin N200,000 ga tsofaffi 250 domin rage musu radadin rayuwa.
Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa uwargidan gwamnan jihar Gombe, Hajiya Asma'u Inuwa Yahaya ce ta jagoranci rabon.
Matar Tinubu ta yi kira ga tsofaffi
Uwargidan Shugaban Kasa ta hori tsofaffin da suka ci gajiyar tallafin da su kula da lafiyarsu ta hanyar cin abinci mai kyau, motsa jiki daidai gwargwado da hutawa yadda ya kamata.
Hakazalika, uwargidan gwamnan Nasarawa ta yaba da kokarin Remi Tinubu, tana kuma kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da kudin yadda ya kamata.
Matar Tinubu ta raba tallafi a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta raba tallafi ga mata a jihar Zamfara a Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mata 1,000 ne suka amfana da tallafin yayin da uwargidan gwamnan jihar Zamfara ta jagoranci shirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng