Kwana Ya Kare: An Shiga Jimami bayan 'Yar NYSC Ta Fadi Ta Mutu a Sansanin Horaswa

Kwana Ya Kare: An Shiga Jimami bayan 'Yar NYSC Ta Fadi Ta Mutu a Sansanin Horaswa

  • An yi jimami a sansanin horar da masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke jihar Kebbi a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Wata matashiyar mai yi wa ƙasa hidima ta riga mu gidan gaskiya bayan fa yanke jiki ta faɗi a sansanin horaswar
  • Kwamishinan matasa da wasanni na Kebbi ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayiyar wacce ta fito daga jihar Adamawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wata mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), wacce aka tura jihar Kebbi, Tayachibiyacha Ebal, ta rasu.

Mai yi wa ƙasa hidiman ta fadi ta mutu ne a sansanin horar da ƴan NYSC da ke Dakin Gari.

'Yar NYSC ta rasu a Kebbi
Mai yi wa kasa hidima ta rasu a Kebbi Hoto: @officialnyscng
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ba zato ba tsammani ƴar NYSC ɗin ta faɗi, inda nan take aka garzaya da ita asibitin sansanin domin kula da lafiyarta.

Kara karanta wannan

"Ku ƙara imani da Allah SWT," Gwamna ya yi magana bayan gobara ta laƙume miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴar NYSC ta mutu a Kebbi

Daga baya aka kai ta babban asibitin FMC da ke Birnin-kebbi, domin ba ta cikakkiyar kulawa.

Sai dai, duk da kokarin da likitocin suka yi na ganin an farfaɗo da ita, marigayiyar ta ce ga garinku nan.

Me hukumomi suka ce kan lamarin

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Sokoto, Alhaji Muhammad Fingila ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Birnin Kebbi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa an aika gawarta zuwa jihar da ta fito watau Adamawa.

Alhaji Muhammad Fingila, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalanta a madadin gwamnatin Kebbi.

A halin da ake ciki, kokarin jin ta bakin jami’an NYSC da ke jihar Kebbi ya ci tura.

Mai magana da yawun NYSC a Kebbi, Misis Hadiza, ba ta amsa kiran da aka yi mata a waya ba, kuma ba ta dawo da amsar saƙon da aka tura mata kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

"Mun ci amanar ƴan Najeriya," Tsohon minista ya bayyana abin da ya faru a mulkin Buhari

Shugaban NYSC ya ɓace

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a jihar Akwa Ibom, Mista Okun Christpoher, ya ɓace ɓat an neme shi an rasa.

Hukumar NYSC ta sanar da cewa an nemi Okun Christopher an rasa ne tare da da direbansa wanda ya ke tuƙa shi a mota lokacin da suke kan hanyar zuwa wurin wani aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng