Majalisa Ta Bukaci Sakin Shugaban Miyetti Allah, ta Gayyaci Hafsun Tsaro
- Majalisar Wakilai ta yi kira ga Hafsun Tsaro, Janar Christopher Musa ya ba da umarnin sakin shugaban Miyetti Allah, Bello Badejo
- 'Yar majalisar tarayya sun ce kama Bello Badejo ba tare da wani izini daga kotu ko gayyata ba ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya
- Haka zalika Majalisar ta yi Allah-wadai da yunkurin sojoji na shiga aikin ‘yan sanda da kotuna wajen warware sabanin jama’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta yi kira ga manyan sojojin Najeriya su gaggauta sakin Shugaban Miyetti Allah, Alhaji Bello Badejo.
Ana zargin cewa Bataliya ta 177 ta Sojin Najeriya ne ta saka aka kama Bello Badejo saboda wani rikici da ya faru kwanakin baya.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa wakilin Darazo/Ganjuwa a Majalisar Wakilai, Mansur Soro ne ya gabatar da kudirin da ya ja hankalin majalisa kan muhimmancin mutunta doka da ‘yancin bil’adama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mansur Manu Soro ya bayyana cewa kama Bello Badejo a Maliya, Jihar Nasarawa, a ranar 9 ga Disamba, 2024, ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Damuwar majalisa kan kama Badejo
Majalisar Wakilai ta bayyana damuwa kan yadda jami’an sojin Najeriya suka kama Bello Badejo ba tare da wani umarnin kotu ko gayyata ba.
Mansur Soro ya ce lamarin ya samo asali ne daga rikici tsakanin wani Janar din soja mai ritaya da wasu jama’ar yankin Maliya.
Majalisar ta kuma nuna damuwa kan yadda tsare Bello Badejo ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba, ke take ‘yancinsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
An bukaci sakin shugaban Miyetti Allah
Daily Post ta wallafa cewa Majalisar Wakilai ta yi kira ga shugabannin tsaron Najeriya su tabbatar an saki Bello Badejo nan take.
Majalisar ta kuma nemi a ba Bello Badejo hakuri kan take masa ‘yancinsa da aka yi ba bisa ka’ida ba.
Majalisa ta gayyaci Hafsun Tsaron Najeriya
Majalisar ta yanke shawarar gayyatar Hafsun Tsaro, Janar Christopher Musa da Kwamandan Bataliya ta 177 su gurfana gaban kwamitocin sojoji, ‘yancin bil’adama da shari’a.
An tsayar da ranar Alhamis, 20 ga Disamba, 2024, karfe 3:00 na rana, domin sauraron dalilin da ya sa jami’ansu suka take kundin tsarin mulkin Najeriya.
An sace makiyaya 11 a jihar Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa makiyaya 11 na kungiyar Miyetti Allah sun yi batan dabo tare da shanu da dama a jihar Anambra.
Legit ta wallafa cewa kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN ta nuna damuwa kan yadda ake jingina makiyaya da ta'addaci ba tare da hujja ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng