Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo da Zancen Kudirin Haraji, Ya Cigaba da Lallabar Jama'a

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo da Zancen Kudirin Haraji, Ya Cigaba da Lallabar Jama'a

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake shaida wa 'yan Najeriya cewa kudirorin gyaran haraji za su taimaki kasa
  • Bola Tinubu ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a Ibadan, inda ya ce bai dace a rika samun matsala a kan batun ba
  • Shugaban kasar na wannan roko ne a lokacin da Arewa ta kafe a kan kin amincewa da kudirin harajin da aka gabatar gaban majalisa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara kare kudurorinsa hudu na gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki ta kasa a halin yanzu.

Ya jaddada cewa an tsara kudurorin, wadanda suka haddasa muhawara mai zafi musamman a yankin Arewa ne domin samun karin kudin shiga a kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya zauna da jagorori, ana son amicewarsu don kudirin haraji ya tabbata

Tinubu
Shugaban kasa ya kare bukatarsa na gyara kudirin haraji Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya bayyana gyare-gyaren harajin a matsayin mataki na karfafa tattalin arzikin kasa da haɓaka kudaden shiga ga gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya nemi goyin baya kan kudirin haraji

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya jaddada bukatar hadin kai a maimakon takaddama tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin ci gaban ƙasa.

Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su goyi bayan kudirorin gyaran harajin da ya ce an tsara su ne don habbaka tattalin arzikin kasa ba muzgunawa kowa ba.

Tinubu zai karfafa alaka da majalisa

Daraktan janar na cibiyar warware rikici a Najeriya, Dr Joseph Ochoku, wanda ya wakilci shugaban kasa a taron da aka gudanar a Jami'ar Ibadan, ya ce kudirinsa zai samar da daidaito.

Da yake magana a madadin shugaba Tinubu, Dr Ochoku ya ce:

"Gwamnatina ta himmatu wajen tabbatar da an samu kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin ci gaban kasarmu."

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

Majalisa na so a amince da kudirin haraji

A wani labarin, kun ji yadda ake samu rahotannin cewa kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya fara tattaro kawunan 'yan majalisa a kan kudirin harajin Bola Tinubu.

Abbas ya gana da Sada Soli daga Arewa maso Yamma; Mukhtar Betara daga Arewa maso Gabas; Ahmed Wase daga Arewa ta Tsakiya da zummar a bar kudirin ya tsallake karatu na biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.