Kama Tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Manyan Nasarorin EFCC da ICPC a Shekarar 2024
- Hukumomin EFCC da ICPC sun kwato fiye da Naira biliyan 277 da Dala miliyan 106 a cikin shekarar 2024 mai karewa
- EFCC ta samu nasarar kwato unguwa mai gidaje 753 da kuma tabbatar da laifuffuka 3,455 a kotuna daban daban
- A halin yanzu, tsofaffin gwamnoni hudu da ministoci uku suna fuskantar shari’a kan zargin rashawa a kotuna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Nigeria - Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa guda biyu a Najeriya, EFCC da ICPC, sun samu gagarumar nasara a shekarar 2024.
Daraktan harkokin shari’a a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce hukumomin sun kwato dukiyoyin da suka kai darajar Naira biliyan 277 da Dala miliyan 106.

Asali: Twitter
The Nation ta rahoto cewa Zakari Mijinyawa ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kwamitin dabarun sadarwa na gwamnati (SCIPC) ya shirya a Abuja ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin EFCC a yaki da rashawa a 2024
Hukumar EFCC ta samu nasarar kwato fiye da Naira biliyan 248 da dala miliyan 105 tare da unguwa mai gidaje 753 kamar yadda Mijinyawa ya bayyana.
Ya kara da cewa EFCC ta samu hukunta masu laifi 3,455 tare da kirkiro sabon sashen kula da damfara da kafa gidan rediyon EFCC 97.3FM domin wayar da kan jama’a.
Har ila yau, hukumar ta samu hadin gwiwa da hukumomi na kasashen waje kamar FBI wajen dawo da dukiyoyin da aka wawure ga wadanda aka zalunta a ketare.
Shari’un EFCC da tsoffin gwamnoni da ministoci
Zakari Mijinyawa ya ce EFCC na ci gaba da shari’ar tsofaffin gwamnoni hudu, ministoci uku, da kuma tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan zargin karkatar da kudi.
Ya ce nasarar EFCC ta nuna jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin tsarin mulki da shari’a a Najeriya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn
Nasarorin da hukumar ICPC ta samu a 2024
A bangarenta, hukumar ICPC ta samu nasarar kwato fiye da Naira biliyan 29 da $9,066 tare da dawo da Naira biliyan 10 daga ma’aikatun gwamnati.
Mijinyawa ya ce kokarin ICPC wajen yaki da cin hanci ya sa Najeriya ta sake samun matsayi a kwamitin jagoranci na GlobE Network, kungiyar duniya da ke yaki da rashawa.
EFCC ta gurfanar da Mama Boko Haram
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gurfanar da Aisha Wakil da aka fi sani da Mama Boko Haram a wata kotu a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
An ruwaito cewa EFCC ta dauki matakin ne kan zargin Mama Boko Haram da wasu mutane biyu da damfarar wata mota mai tsadan gaske.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng