An Cafke Masu Lalata Turakan Lantarki a Najeriya Suna Kokarin Kafka Barna
- Kamfanin rarraba wuta na TCN ya kama mutane shida bisa zarginsu da lalata manyan hasumiyar wutar lantarki a Ribas
- Jami’an TCN sun bayyana cewa wadanda ake zargin suna da hannu wajen lalata manyan kayayyakin lantarki a kasar nan
- TCN ya bayyana matakin da zai dauka a kan mutanen domin su kasance abin ishara ga sauranmasu lalata kayan lantarki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da kama wasu mutane da ake zargi da lalata hasumiyar wutar lantarki a jihar Ribas.
Babban manajan yankin Fatakwal na kamfanin, Injiniya Emmanuel Anyaegbulam Akpa ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin.

Source: Getty Images
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Emmanuel Anyaegbulam Akpa ya ce za su dauki mataki a kan wadanda ake zargin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana hasashen da mutanen sun samu nasara, gaba dayan jihar za ta fada cikin duhu, kuma dawowa da wutar zai ci lokaci da kudi masu yawa.
Kamfanin TCN ya kama masu lalata turakan lantarki
Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa TCN ya kama wasu mutane shida da ke yunkurin rusa turakan lantarki a Ribas.
Injiniya Akpa ya bayyana cewa mutanen da aka kama sun kasance cikin jerin wadanda suka dade suna lalata hasumiyar wutar lantarki da sauran muhimman kayayyakin TCN a jihar.
TCN za ta gurfanar da mutane 6 a gaban kotu
Manajan kamfanin a Fatakwal ya ce akwai mutane hudu da ake tuhuma a baya kuma suna fuskantar shari’a kan laifuffukan lalata kayayyakin TCN.
Punch ta wallafa cewa Injiniya Akpa ya ce sababbin mutum shida da aka kama za su gurfana a kotu nan ba da jimawa ba domin su fuskanci hukunci.
An lalata turken wutar lantarki a Bayelsa
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wuta na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa wasu miyagu sun lalata turken wuta a jihar Bayelsa.
Legit ta rahoto cewa bata garin sun kai hari ne kan layin wutar lantarki na Ahoada-Yenagoa 132kV, suka jefa al'ummar da ke kan layin wutar a duhu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

