Taraba: Faɗa Ya Kaure tsakanin Masu Ibada, Mutum 3 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya
- Akalla mutum uku sun rasa rayukansu yayin da faɗa ya kaure tsakanin mabiyan cocin UMCN da cocin GMC a jihar Taraba
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ya ce an tura jami'an tsaro zuwa yankin don tabbatar da tsaro
- An ruwaito cewa rikicin ba sabo ba ne, tsohuwar takaddama ce kan shugabanci wadda ta kai ga rufe hedkwatar UMCN a Jalingo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - 'Yan sanda a jihar Taraba sun tabbatar da mutuwar mutane uku a wani rikici da ya barke tsakanin masu ibada a coci guda biyu.
Faɗan ya kaure ne tsakanin mabiyan cocin UMCN ta Najeriya da masu ibada a cocin GMC, wanda ta kai ga rasa rayuka a Taraba.
Yadda faɗa ya kaure tsakanin coci 2
Daily Trust ta tattaro cewa rikicin ya samo asali daga wata tsohuwar tsama da ke tsakanin mabiya cocin biyu wanda ya sa gwamnati ta rufe hedkwatar UMCN a Jalingo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ya ce rikicin ya faru ne a karamar hukumar Karim-Lamido tsakanin mabiya cocin biyu ranar Lahadi.
SP Usaman ya bayyana cewa zuwa ƴanzu ƴan sanda sun cafke mutum shida da ake zargi da hannu a tayar da rikicin.
Ya kara da cewa an tura dakarun ‘yan sanda da sojoji domin hana sake ɓarkewar wani faɗan tsakanin masu ibadar.
Abin da ya hawo rikicin masu ibada
Wasu ƙarin bayanai da aka tattara sun nuna cewa faɗan ya kaure ne kan tsohuwar rigimar shugabanci a tsakanin cocin UMCN da GMC.
A kwanakin baya gwamnatin Taraba ta rufe hedkwatar UMCN da ke Jalingo kan wannan rikicin, amma duk da haka wasu bara gurbi suka sake tayar da shi.
Rikicin dai shi ne ya jawo wasu daga cikin mabiyan cocin suka ɓalle suka kafa tsaginsu, hakan ya sa alaƙa ta yi tsami tsakanin ɓangarorin biyu.
Kakakin ƴan sanda ya tabbbatar da cewa mutum uku sun mutu a sabon faɗan da ya kaure amma ak tura jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Cocin RCCG ta dakatar da fastoci 2
A wani rahoton, an ji cewa cocin RCCG ta dakatar da wasu malamai biyu bisa zarginsu da neman maza wanda ya saɓawa littafi mai tsarki.
A wata sanarwa da cocin ta fitar, ta ce ta dakatar da su ne domin gudanar da bincike kan zargin da ake masu.
Asali: Legit.ng