'Yan Sanda Sun Dauki Mataki bayan An Yi Musu Tayin Cin Hancin N66m
- Jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Legas sun yi abin a yaba bayan sun tsallake tayin cin hancin N66m da aka yi musu
- Ƴan sandan sun cafke mutanen ne waɗanda suka ƙware wajen aikata damfara duk da tayin da suka yi ba da na goro
- Jami'an Zone-2 da ke Legas ko a watan Nuwamban da ya gabata sun ƙi ƙarɓar tayin cin hancin N174m daga wani mai laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Rundunar ƴan sanda ta Zone-2 da ke Legas ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifukan damfara.
Ƴan sandan sun cafke mutanen guda biyu da ake zargi da hannu wajen yin jabun satifiket na ƙasashen waje a Legas da Ghana.
Ƴan sanda sun tsallake cin hancin N66m
AIG Adegoke Fayoade, wanda ke shugabantar rundunar ƴan sanda ta Zone-2, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani abin a yaba da ke nuna gaskiyarsu, ƴan sandan sun ƙi karɓar tayin cin hancin Naira miliyan 66 daga hannun waɗanda ake zargin.
"Waɗannan waɗanda ake zargin, Elvis, mai shekara 23, da Kelly, mai shekara 24, sun ƙware wajen yin takardun satifiket na jabu na makarantun ƙasashen waje da jami’o’in Afirka, suna yaudarar waɗanda ba su ji ba gani a yanar gizo."
- Adegoke Fayoade
Ƴan sanda sun ƙi karɓar N174m a watan Nuwamba
Rundunar ƴan sanda ta kuma ƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 174 a watan Nuwamba daga wani wanda ake zargi da yunƙurin kaucewa shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun tara dukiya ta haramtacciyar hanya, inda suka mallaki motoci na alfarma da kadarori a faɗin ƙasar nan.
Ƴar sandar Najeriya ta kafa tarihi a duniya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata jami'ar ƴan sandan Najeriya mai suna Juliet Chukwu ta kafa tarihi a fagen wasanni bayan ta shiga wata gasa da aka yi.
Jami'ar ƴan sandan ta samu nasarar lashe kambun Bantamweight na gasar damben EFC119 wanda aka gudanar a birnin Johannesburg a ƙasar Afirika ta Kudu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng