Gwamnatin Tinubu Za Ta Wuce Gona da Iri, Bashin da Aka Karbo Ya Haura Iyaka da N4trn

Gwamnatin Tinubu Za Ta Wuce Gona da Iri, Bashin da Aka Karbo Ya Haura Iyaka da N4trn

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 da yawansa ya kai Naira tiriliyan 47.9
  • A wannan adadi, gwamnatin tarayya za ta karbo rancen Naira tiriliyan 13.8 domin yin ciko ga kasafin kudin da aka tsara
  • Bincike ya tabbatar da cewa zuwa yanzu, gwamnati ta karbi bashin da ya wuce adadin da aka tsara za ta karba a watanni 11

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Yayin da shugaba Bola Tinubu ke shirin gabatar da kasafin kudin kasa 2025 a gaban Majalisar kasar nan a ranar Talata, mafi yawan kasafin kudin ta hanyar aro za a samu.

A yanzu haka, gwamnati na dab da zarce tsarinta na aron cikin gida na 2024 da Naira tiriliyan 4, kimanin 67%, wanda ya haura adadin da aka tsara.

Kara karanta wannan

'Saurin me ake yi?" Dattawan Arewa sun shawarci gwamnati kan kudirin harajin Tinubu

Bola Tinubu
Gwamnati na wuce gona da iri wajen karbo rance Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Binciken da ya kebanta da jaridar Vanguard ya nuna cewa wannan na faruwa duk da damuwar da ake ta bayyana wa game da ci gaba da cin bashi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta haura adadin bashin da ya dace

Bayanan gwamnati a kan rancen cikin gida daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2024 sun nuna cewa an riga an karbi aron Naira tiriliyan 2.93.

Wannan ya wuce abin da aka tsara, ko kuma karin 49% na rancen da gwamnati ya dace ta karba daga farkon shekarar nan zuwa watan Nuwamba.

Gwamnatin Najeriya ta karbi bashin N8.93trn

Binciken ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta karbi aron Naira tiriliyan 8.93 daga masu zuba jari na cikin gida a cikin watanni 11 wanda ya zarce Naira tiriliyan 6 da aka iyakance.

Idan wannan yanayi ya ci gaba a haka, akwai yiwuwar gwamnatin tarayya za ta karbi aron Naira tiriliyan 10 a 2024, wanda zai haura adadin da aka amince ta karba da 67%.

Kara karanta wannan

Na farko a Arewa: Gwamna ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 1.5

Jihohin Najeriya sun rake karbo rance

A baya, mun ruwaito cewa rahoton ofishin kula da basussukan kasar nan ya tabbatar da cewa jihohi sun rage yawan bashin da su ke karbo wa a cikin gida da kaso mai tsoka.

Alkaluman da ofishin ya fitar ya nuna cewa jihohin Arewa maso Gabas ne kan gaba wajen rage basussukan da 95%, wanda ya kai Naira Biliyan 40.69 daga Janairu zuwa Maris.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.