Yaki da 'Yan Bindiga: Manyan Arewa Sun Halarci Kaddamar da Askarawa 5,000

Yaki da 'Yan Bindiga: Manyan Arewa Sun Halarci Kaddamar da Askarawa 5,000

  • Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya jagoranci gwamnonin Arewa wajen kaddamar da askarawa 5,000 a jihar Benue
  • Rahotanni sun nuna cewa an ƙaddamar da sababbin motocin aiki da babura domin aiki da su wajen yaki da 'yan bindiga a jihar
  • Manyan shugabanni ciki har da wakilan gwamnatin tarayya da na jihohin Arewa sun halarci taron ƙaddamar da askarawan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Shugaban gwamnonin Arewa kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga haɗin kai da tallafa wa shirin tsaro a jihar Benue.

Kiran ya biyo bayan halartar gwamna Inuwa Yahay taron ƙaddamar da askarawa a Makurdi, babban birnin jihar Benue a matsayin babban bako na musamman.

Asakarawa
An kaddamar da asakarawa a Benue. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa Inuwa Yahaya ya ce shirin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan jirgin ruwa ya kife da fasinjoji a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Inuwa Yahaya ya yabi shirin tsaron Benue

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana jin daɗinsa ga Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue bisa tsarin ƙirƙirar askarawa a matsayin sabuwar hanyar yaki da rashin tsaro.

A jawabinsa, Inuwa Yahaya ya ce tsaro ne ginshiƙin ci gaba, inda ya bayyana cewa ba za a iya cimma nasara a komai ba idan babu shi.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Benue cewa za su cigaba da samun goyon bayan gwamnonin Arewa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Yadda aka kaddamar da askarawa a Benue

Taron ya samu halartar manyan baƙi ciki har da wakilin shugaba Tinubu, Ibrahim Kabir Masari, gwamnan Yobe, Abdullahi Umar Ganduje da wakilan shugaban 'yan sanda na ƙasa.

A lokacin taron, an ƙaddamar da askarawa 5,000, tare da mika sababbin motoci guda 100 da babura 600 ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da wasu gwamnoni ana tsaka da surutu kan ƙudirin Haraji

Tor Tiv ya yabi jagorancin gwamnonin Arewa

Mai martaba Tor Tiv, Farfesa Ortese Iorzua James Ayatse, ya yaba wa gwamna Inuwa Yahaya bisa ƙoƙarinsa na jagorantar gwamnonin Arewa yadda ya kamata.

Daily Trust ta wallafa cewa basaraken ya ce an samar da askarawan ne ba tare da wata manufa ta siyasa ba.

Gwamna Alia ya gode wa duk manyan baƙin da suka halarci taron, musamman Gwamna Inuwa Yahaya kan goyon bayansa ga shirin tsaron jihar Benue.

An kaddamar da askarawa 500 a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yaye askarawa kimanin 500 domin yaki da 'yan bindiga.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya halarci taron inda ya bayyana cewa an tanadi dukkan kayan aiki ga asakarawan domin inganta tsaron jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng