Shekarau Ya Yi Hangen Nesa, Ya ba Gwamnatin Tinubu Shawara
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya taɓo batun fitowa kan tituna da ƴan Najeriya suka yi a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance
- Ibrahim Shekarau ya ce hizanga-zangar da ƴan Najeriyan suka fito suka yi, saƙo ne ƙarara ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu
- Tsohon gwamnan ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta tsaya ta sake duba yadda take tafiyar da ragamar jagorancin mutanen Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi tunatarwa ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Ibrahim Shekarau ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta koma ta yi karatun ta natsu kan yadda take mulkar talakawa.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Shekarau ya ba Tinubu?
Shekarau ya bayyana cewa zanga-zangar #EndBadBadGovernance da aka gudanar a kwanakin baya, saƙo ne ƙarara ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
"Zanga-zangar ƙarshe da aka yi kan #EndBadGovernance saƙo ne ƙarara. Fushin ba na yanki ba ne, ba na jiha ba ce, abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaƴa."
"Ina tunanin wannan saƙo ne ƙarara ga shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya. Ƴan Najeriya na cewa ku koma ku sake shiri, ku ƙara duba abubuwan da kuke yi mana."
- Malam Ibrahim Shekarau
Ƴan Najeriya sun yi zanga-zanga
A farkon watan Agustan 2024 ne dai ƴan Najeriya suka fito kan tituna domin nuna adawarsu kan yadda abubuwa suka taɓarɓare a ƙasar nan.
Ƴan Najeriya sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta sauya wasu daga cikin manufofinta kamar cire tallafin man fetur, wanda ya tsunduma mutane cikin wahala.
Shekarau ya ba ƴan Najeriya shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya bayyana ɗan takarar da ya kamata ƴan Najeriya su ba ƙuri'unsu a zaɓen 2027.
Shekarau ya bayyana cewa ya kamata ƴan Najeriya su kawar da kansu daga kallon yankin da ɗan takara ya fito, inda ya ce nagarta ya kamata su duba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng