Badenoch: Igboho Ya Bukaci Tinubu Ya Ja Kunnen Shettima kan Sukar Bayarbiya
- Dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo ya roki Bola Tinubu ya ja kunnen mataimakinsa, Kashim Shettima
- Adeyemo da ake kira da Sunday Igboho yana magana ne kan sukar Kemi Badenoch da Shettima ya yi kan fadan gaskiya
- Hakan ya biyo bayan caccakar tsarin Najeriya da kuma Arewa da shugabar jam'iyyar Conservative ta Birtaniya ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Mai fafutukar kafa ƙasar Yarbawa, Sunday Adeyemo ya bukaci Bola Tinubu ya takawa mataimakinsa birki.
Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi kira ga Tinubu da ya gargaɗi Kashim Shettima kan sukar shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya, Kemi Badenoch.
Maganar Badenoch da ta jawo ka-ce-na-ce a Najeriya
Punch ta ruwaito cewa Badenoch ta rikita kafofin sadarwa inda ta ke sukar Najeriya da yadda hukumominta suke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yar siyasar daga bisani ta barranta kanta da Najeriya musamman Arewacin Najeriya da ta ce gidan Boko Haram ne da ta'addanci.
Sai dai Kashim Shettima ya caccake ta inda ya gargade ta kan bata sunan Najeriya yayin da take Burtaniya.
Maganar Badenoch ta samu yabo da kuma suka daga wasu a Najeriya haka ma martanin Shettima.
Sai dai Igboho a bangarensa a cikin wata sanarwar ya bukaci a takawa Shettima birki kan sukar Badenoch saboda tana da gaskiya, cewar Tribune.
“Yana da muhimmanci Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ma 'dan asalin yankin Yarbawa ne, ya umurci Shettima ya mayar da hankali kan ayyukansa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa."
"Hakan zai fi masa maimakon shiga rikicin magana da Badenoch da ke ketare wacce kuma gaskiya ta fada."
- Sunday Igboho
Igboho ya fadi manyan matsalolin Najeriya
Igboho ya soki gwamnati da gazawa wajen magance matsalolin da ke addabar 'yan kasar, daga cikin matsalolin har da matsin tattalin arziki da talauci da rashin tsaro.
Ya roƙi Tinubu da ya shiga tsakani domin tabbatar da cewa Kashim Shettima ya daina yi wa Badenoch suka marasa amfani.
Shettima ya ce tattalin arziki na bunƙasa
Kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta ce yanzu haka tattalin arzikin Najeriya ya fara hawa turbar bunkasa kamar yadda ake so.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci bude kasuwar duniya a Lagos.
Asali: Legit.ng