Kano: Jarumin Kannywood, Sani Danja Ya Samu Babban Mukami a Gwamnatin Abba
- Jarumi Sani Danja ya samu mukamin babban mai ba da shawara na musamman ga gwamnan Kano kan matasa da wasanni
- Ana ganin wannan nadin ya biyo bayan gagarumin kokarin Sani Danja wajen inganta harkokin matasa da wasanni a Kano
- 'Yan Kannywood sun fito sun taya Sani Danja murna tare da addu'o'in nasara a sabon mukamin da ya samu a gwamnatin Abba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Masana'antar Kannywood ta cika da murna a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba yayin da Sani Danja ya samu babban mukami a gwamnatin Kano.
Jarumi Sani Danja, na daga cikin mutane 12 da Gwamna Abba Yusuf ya nada mukamai kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature ya sanar.
Abba ya yiwa Sani Danja nadin mukami
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kanon ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce Abba ya nada Sani Danja matsayin babban mai ba shi shawara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Sanusi Bature ta nuna cewa Sani Danja zai rika ba Gwamna Abba Yusuf shawara kan harkokin matasa da wasanni.
Wannan nadin mukamin dai na zuwa ne watanni bayan da Sani Danja ya rasa kujerar ciyaman na karamar hukumar Nassarawa da ya nema karkashin jam'iyyar NNPP.
Sanarwar ta ce nade naden da gwamnan ya yi za su fara aiki nan take.
'Yan Kannywood sun taya Danja murna
Legit Hausa ta tattaro sakonnin taya murna da jaruman Kannywood suka aikawa Sani Danja bayan samun wannan mukami.
"Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusif ya naɗa Sani Danja a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni."
"Hakuri mai tadda rabo.
"Hon. Sani Musa Danja
"Babban mai ba da shawara na musamman kan matasa da wasanni
"Sai godiya Abban Kanawa."
"Ina taya ka murna dan uwana @realsanidanja, Allah ya taya riko. Ameen."
alhajisheshe:
"Ina taya ka murna @realsanidanja, Allah ya yi riko da hannayenka."
"Muna taya murna Baban iman @realsanidanja."
Abba ya yi sababbin nade nade
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya yi sababbin nade nade a gwamnatinsa tare da sauya wa wasu jami'ai wurin aiki.
Wannan dai na daga cikin matakin da gwamna ya ke ci gaba da dauka na yin garambawul a gwamnatinsa da nufin inganta harkokin gwamnati na yiwa al'umma aiki.
Asali: Legit.ng