Gwamna Abba Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa, Sani Danja Ya Samu Mukami

Gwamna Abba Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa, Sani Danja Ya Samu Mukami

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa kwanaki kaɗan bayan korar wasu kwamishinoni
  • Abba Kabir Yusuf ya naɗa masu ba da shawara na musamman da shugabannin wasu hukumomin gwamnati
  • Daga cikin waɗanda suka samu muƙamin akwai jarumin masana'antar Kannywood, Sani Musa Danja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.

Gwamna Abba ya kuma amince da sauya wurin aiki ga shugabannin wasu hukumomi da masu ba da shawara na musamman.

Gwamna Abba ya yi rabon mukamai
Gwamna Abba ya sababbin nade-nade Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani Danja ya samu muƙami a gwamnatin Abba

Daga cikin sababbin mutanen da aka naɗa akwai fitaccen likita, Dakta Ibrahim Musa, na asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), da kuma fitaccen jarumin Kannywood, Sani Musa Danja.

Kara karanta wannan

An daura auren fitaccen mawakin Kannywood: Ado Gwanja, Hamisu Breaker sun halarta

Ga jerin mutanen da aka naɗa da wuraren da za su yi aiki:

1. Dr. Ibrahim Musa - Mai ba da shawara na musamman, harkokin kiwon lafiya, likitan gwamna.

2. Dr. Hadiza Lawan Ahmad - Mai ba da shawara ta musamman kan zuba jari.

3. Sani Musa Danja - Mai ba da shawara na musamman, matasa da wasanni.

4. Barr. Aminu Hussain - Mai ba da shawara na musamman kan harkokin shari'a da kundin tsarin mulki.

5. Dr. Ismail Lawan Suleiman - Mai ba da shawara na musamman, yawan Jama’a.

6. Nasiru Isa Jarma - Mai ba da shawara na musamman, ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs).

7. Hon. Wada Ibrahim Daho - Kwamishinan dindindin na I, SUBEB

8. Hon. Ado Danjummai Wudil - Shugaban hukumar gyara tarbiyya da ba da shawarwari

9. Dr. Binta Abubakar - Shugabar hukumar Ilimin manya

10. Hon. Abubakar Ahmad Bichi - Darakta janar, hukumar kula da masu sana'o'i a bakin titi

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Uba Sani ya ba da sabon mukami a gwamnatinsa

11. Hon. Abdullahi Yaryasa - Mamba hukumar kula da majalisar dokoki.

12. Dr. Yusuf Ya’u Gambo - Shugaba 'Strategic Governance and Policy Coordination'.

Sanarwar ta bayyana cewa naɗin na su zai fara aiki ne nan take.

Gwamna Abba ya yi kora

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya runtuma kora bayan ya yi garambawul a gwamnatinsa.

Gwamnan na jihar Kano ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa yayin da sauyawa wasu ma'aikatun da za su jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng