An Samu Asarar Rayuka bayan Jirgin Ruwa Ya Kife da Fasinjoji a Jihar Arewa

An Samu Asarar Rayuka bayan Jirgin Ruwa Ya Kife da Fasinjoji a Jihar Arewa

  • Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya gamu da hatsari a ƙaramar hukumar Agatu da ke jihar Benue a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Jirgin ruwan dai ya gamu da hatsarin ne a daren ranar Asabar bayan mutanen da ke cikinsa sun kammala cin kasuwa
  • Shugaban ƙaramar hukumar Agatu ya bayyana cewa an gano gawarwakin kusan mutane 20 yayin da ake ci gaba da aikin ceto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - An samu asarar rayuka bayan wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi hatsari a jihar Benue.

Rahotanni sun ce sama da mutane 20 ne suka mutu a daren ranar Asabar, a hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a a ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benue.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Benue
Jirgin ruwa ya kife da fasinjoji a Benue Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yawancin waɗanda abin ya shafa ƴan kasuwa ne.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa 'yan bindiga kwanton bauna, sun tura miyagu zuwa barzahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Benue

Mutanen dai suna kan hanyar komawa gidajensu ne bayan tashi daga kasuwar Ocholonya da ke ƙaramar hukumar Agatu, rahoton Tribune ya tabbatar.

"Mutanen da abin ya shafa sun kasance ƴan Agatu ne daga ƙananan hukumomin Toto da Doma a jihar Nasarawa waɗanda suka zo kasuwar Ocholonya ranar Asabar."
"An yi wa kwale-kwalen na katako lodin da ya fiye ƙima, kuma duk da gargadin da aka yi cewa wasu fasinjojin su sauka, ba a ji ba domin suna gaggawar komawa gida.
"Ana tsakiyar tafiya ne kwale-kwalen ya ɓalle bayan ya bugi wata bishiya, lamarin da ya sa da yawa daga cikin fasinjojin suka nutse."
"Masu iyo a yankin sun ciro wasu gawarwaki, amma da yawa sun ɓace."

- Wani ganau

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Mista Melvin Ejeh, ya bayyana cewa kawo yanzu an gano gawarwaki kusan 20, kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan fashewar wani bam a Borno, bayanai sun fito

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, ASP Catherine Anene tabbatarwa da Legit Hausa aukuwar lamarin

ASP Catherine Anene ta bayyana cewa mutum 10 ne suka rasu yayin da aka samu nasarar ceto mutum 11.

"Eh lamarin ya auku. Mutum 10 sun rasu yayin da aka ceto nutum 11. Ana ci gaba da aikin ceto."

- ASP Catherine Anene

Jirgin ruwa ya kife da ƴan Maulidi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu wani hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da ƴan Maulidi a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Hatsarin wanda ya faru a ƙaramar hukumar Mokwa, ya ritsa da mutane 300 waɗanda suke tafiya zuwa wajen taron Maulidi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng