PDP Ta ba Jonathan Damar Gwabzawa da Tinubu a 2027? Jam'iyyar Ta Yi Bayani
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi magana kan rahotannin da ke cewa tana zawarcin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan
- PDP ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta zawarcin tsohon shugaban ƙasan na Najeriya domin shi ɗan jam'iyyar ne
- Ta kuma musanta cewa ta ba shi tikitin yin takara a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta yi martani kan batun son Goodluck Jonathan ya yi takara a ƙarƙashinta a shekarar 2027.
Jam'iyyar PDP ta musanta rahotannin waɗanda suke cewa tana zawarcin tsohon shugaban ƙasan domin ya yi takara a zaɓen 2027.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Ibrahim Abdullahi, ya musanta hakan yayin wata tattaunawa da jaridar BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta musanta ba Jonathan tikitin takara
Ibrahim Abdullahi ya musanta cewa PDP ta ba Goodluck Jonathan tikitin takara a zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa rahoton cewa PDP ta ba Jonathan tikitin takararta ko tana kira a gare sa da ya zo ya yi takara, babu gaskiya a cikinsa.
Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa babu yadda za a yi su yi zawarcin Jonathan, domin shi ɗan jam'iyya ne, kuma PDP ta yi masa komai.
Ya ƙara da cewa ko tattauna batun yin takara ba su yi ba da Jonathan, kuma ba shi kaɗai ba ne wanda zai iya yin takara ƙarƙashin inuwar PDP.
"Abin da ya faru ni ne ɗin nan na yi hira da ɗan jarida, muna hira a kan wasu maganganu daban, sai a cikin hirar ya ambato tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cewa mene ne tunaninmu a kansa?"
"Ana kira ya zo ya yi takarar shugaban ƙasa. Ƴan Najeriya na kira. Shi ne na amsa masa da cewa babu shakka ya cancanci ya yi tun da ɗan Najeriya ne kuma yana da damar ya yi haka a fuskar doka kuma yana da wa'adi ɗaya na takarar shugaban ƙasa."
"So fitowarsa ya yi takara ba illa ba ne a zamansa ɗan Najeriya kuma babu abin da ya hana shi yin haka a idon doka."
- Ibrahim Abdullahi
Fastocin Jonathan sun fara yawo a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara ganin fastocin kamfen na tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a birnin Kano.
Ƙungiyar TNT wacce ke kan gaba wajen sanya fastocin, na son ganin Jonathan ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng