Tinubu Ya Shiga Matsala da Ake Zargin an Handame N57bn a Ma'aikata, Ana Tuhumarsa
- Kungiyar SERAP ta maka Bola Tinubu a gaban kotu kan badakalar N157bn a ma'aikatar jin kai da walwala
- Kungiyar ta bukaci kotu ta tilasta Tinubu umartar fara bincike da hukunta masu laifi idan akwai hujjoji
- Wannan na zuwa ne bayan fitar da rahoton cewa an handame kudin a ma'aikatar a cikin shekarar 2021 kadai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin jama’a da tabbatar da adalci, SERAP ta maka Bola Tinubu a gaban kotu.
Kungiyar SERAP ta shigar da kara a gaban kotu kan Tinubu saboda barin badakalar N57bn a ma'aikatar jin kai da walwala ba tare da bincike ba.
Badakalar N57bn: SERAP ta maka Tinubu a kotu
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafin X a yau Lahadi 15 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar na tuhumar Tinubu kan kin umartar Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya hada kai da hukumomin yaki da rashawa don binciken zargin batan kudaden.
Kungiyar SERAP ta ce abin takaici ne yadda makudan kudi har N57bn za su bace a ma'aikatar jin kai da walwala a cikin shekarar 2021 kadai
Wadannan zarge-zarge masu nauyi sun fito ne daga rahoton kididdigar kudi na shekarar 2021 da ofishin mai binciken kudi na Tarayya ya fitar.
Kungiyar ta sanya sunan Lateef Fagbemi a cikin karar a matsayin wanda ake kara.
'Abin da ya kamata Tinubu ya yi' - SERAP
Har ila yau, SERAP tana kuma neman kotu ta tilastawa Tinubu ya umarci Ministan da hukumomin da abin ya shafa su gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a batan kudin.
Sannan a kwato duk wasu kudaden da suka bace idan akwai hujjoji masu karfi da suka tabbatar da hakan.
“Binciken zarge-zargen da gurfanar da wadanda ake zargi tare da kwato kudaden da suka bace zai kawo karshen rashin hukunci ga wadanda suka aikata wannan laifi.”
“Wadannan zarge-zarge na nufin sace dukiyar talakawa ne, muradin jama’a ne ganin an samu adalci kan wadannan zarge-zargen masu girma.”
- Cewar SERAP
Kudin mai: SERAP ta ba Tinubu wa'adi
Kun ji cewa Kungiyar SERAP ta ba Shugaba Bola Tinubu wa'adin awanni 48 da ya umarci kamfanin NNPCL ya gaggauta janye karin kudin man fetur da ya yi.
Bayan bukatar janye karin kudin man, SERAP ta kuma bukaci Tinubu da ya ba Ministan shari'a da hukumomi umarnin bincikar NNPCL.
Asali: Legit.ng