Karanci Kudi: CBN Ya Gano Masu Jawo Matsalar, Ya Fadi Tarar da Zai Ci Bankuna
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ana yawan korafi kan ƙarancin kudi a bankuna a mafi yawan jihohin Najeriya
- Hakan bai rasa nasaba da zargin bankuna da fifita wasu masu hulda da su kan sauran al'umma
- Ganin haka, bankin CBN ya yi bincike da kuma kakaba wasu matakai da tara kan wasu bankuna masu aikata haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya, CBN ya gano wadanda suke jawo karancin kudi a hannun al'umma.
Bankin ya bayyana haka ne bayan wani bincike da ya gudanar yayin da ake fama da ƙarancin kudi.
Karancin kuɗi: Bankin CBN ya zargi bankuna
The Nation ta tabbatar cewa CBN ya zargi bankunan da ba manyan masu hulda da su kuma masu ido da kwalli kudi fiye da sauran mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki na ba manyan masu hulda da su kudaden ya jefa sauran mutane da kananan yan kasuwa cikin mummunan yanayi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa CBN ya dauki matakin ladabtar da duk bankin da aka samu da laifin.
Daga cikin hukuncin shi ne kakaba tarar N150m ga duk bankin da aka samu da fifita wasu kan sauran al'umma.
Sannan CBN zai sanya ido kan hulɗar bankuna da masu sana'ar POS wurin samar musu da kudi.
An tabbatar da cewa masu POS na samun fifiko kan sauran masu mu'amala da bakuna wurin rattaba musu kudaden.
Bankin CBN ya ba al'umma shawara kan haka
Daga bisani CBN ya shawarci al'umma da suka fuskanci wannan bambanci su kai rahoto ta hanyar da ya dace.
Bankin ya bukaci ba da bayanai masu muhimmanci domin saukin samun wadanda ake korafi.
Yayin da ake shirin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara mutane suna bukatar kudi sosai domin yin siyayya.
Sai dai hakan na cigaba da zama matsala musamman a lokacin da aka fi bukatar hakan, cewar rahoton Punch.
Legit Hausa ta tattauna da mai sana'ar POS
Wani mai sana'ar POS ya fadawa Legit Hausa yadda yake samun kuɗi saboda harkokin kasuwancinsa.
Abubakar Mohammed Madaki ya ce tabbas ana shan wahala wurin samun kuɗi a banki amma shi a kasuwancinsa yake cirewa ya yi amfani da su.
"Tabbas akwai wadanda ake ba kudi musamman a banki saboda suna sana'ar POS."
"Amma ni ina kasuwanci mafi yawan lokuta daga ciki cirewa nake amfani da su wurin sana'a ta."
- Abubakar Mohammed Madaki
CBN ya magantu kan tsofaffin takardun Naira
Mun ba ku labarin cewa, Bankin CBN ya bukaci ƴan Najeriya su yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa cewa za a daina amfani da tsofaffin kuɗi nan kusa.
Bankin CBN ya tabbatar cewa babu ranar daina amfani da kowane irin takardun kudi, tsoho ko sabo duba da hukuncin da kotun koli ta yanke.
Asali: Legit.ng