Rusau a Jihar Kano Ya Jawo ‘Dan Kasuwa Zai Kai Karar Hukumar KNUPDA a Kotu

Rusau a Jihar Kano Ya Jawo ‘Dan Kasuwa Zai Kai Karar Hukumar KNUPDA a Kotu

  • Ibrahim Mukhtar ya yi hira da manema labarai yana mai kukan yadda aka rusa masa gidan cin abinci
  • ‘Dan kasuwan zai iya shiga kotu da hukumar KNUPDA a sakamakon ruguza gininsa da ke unguwar Gandu
  • Shugaban KNUPDA ya yi watsi da zancen Ibrahim Mukhtar, ya ce ginin da ya yi ya sabawa dokokin Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Ibrahim Mukhtar wanda ‘dan kasuwa ne, zai iya yin shari’a da gwamnatin jihar Kano a sakamakon rusa masa dukiya.

Ibrahim Mukhtar ya yi ikirarin gwamnatin Kano ta ruguza masa wurin neman abinci, ba yau aka saba irin wannan aiki a jihar ba.

Rusau a Kano
'Dan kasuwa ya zargi hukumar KNUPDA da rusau ba tare da ka'ida ba a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf/solacebase.com
Asali: UGC

Ibrahim Mukhtar ya yi kuka da KNUPDA

Labarin da aka samu daga Daily Nigerian ya bayyana cewa Ibrahim Mukhtar ya yi barazanar shigar da karar KNUPDA a gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan kasuwan ya ce hukumar KNUPDA mai alhakin kula da gine-gine a jihar Kano ta rusa masa wurinsa da ke Alhamsad Tower a Gandu.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya goge raini, ya tabbata mai kudin duniya da dukiyarsa ta kai $447bn

A cewarsa, ranar Litinin da ta gabata aka rusa ginin da aka kammala, yake cewa KNUPDA ba ta bi ka’idojinta a wajen wannan aiki ba.

KNUPDA ta ba shi izinin yin ginin a Kano?

Kafin ya yi ginin, Ibrahim Mukhtar ya ce sai da ya nemi izini daga hukumar kuma aka yi masa izini ya gina wurin cin abinci a yankin.

Ana zaune kwatsam, Mukhtar ya ce jami’an hukumar KNUPDA suka rusa wannan wuri ba tare da sun aiko masa da wata takarda ba.

Da ya tara manema labarai a karshen makon nan, an ji shi yana cewa ya yi bakin cikin ganin yadda aka rusa kyakkyawan ginin nasu.

‘Dan kasuwar ya ce ya gina wurin cin abincin ne saboda ya taimakawa yara su samu na kashewa, ba don shi ya tara abin duniya ba.

Hukumar KNUPDA ta yi magana

Solacebase ta ce da aka tambayi shugaban hukumar KNUPDA, Ibrahim Yakubu Adamu, sai ya ce ginin ya tare hanya kuma bai kan ka'ida.

Kara karanta wannan

'Ba ku da hankali ne': Akpabio ga masu fada da Ministan Tinubu, ya jero dalilansa

Ibrahim Yakubu Adamu ya musanya maganar ‘dan kasuwar, ya ce sai da suka ja masa kunne tun watan Yuli kafin su kai ga rushe ginin.

Duk da ya biya kudi yana mai neman izini, KNUPDA ta ce bai samu amincewar hukuma ba tukuna, don haka ginin ya sabawa ka’ida.

Hadimin gwamnan Kano ya yabi Bichi

A baya an rahoto cewa Mai taimakawa gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro, ya yi magana a kan tsige Abdullahi Baffa Bichi da aka yi.

Hadimin gwamnan ya ce ya so Allah SWT ya bar Bichi da cikakkiyar lafiya da kwarin jiki ya yi aiki a matsayin sakataren gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng