Shugaban INEC Mahmood Yakubu Ya Rasu? An Gano Abin da Ya Faru

Shugaban INEC Mahmood Yakubu Ya Rasu? An Gano Abin da Ya Faru

  • Wasu rahotanni sun yaɗu kan rasuwar shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu
  • Hukumar INEC ta fito ta musanta rahotannin waɗanda ta bayyana a matsayin tsantsagwaron ƙarya da ƙarairayi
  • Ta buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da rahotannin, inda ta ce Mahmood Yakubu yana cikin ƙoshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta yi magana kan batun cewa shugabanta Farfesa Mahmood Yakubu ya rasu.

Hukumar INEC ta musanta rahotannin da ke yawo masu cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya yi bankwana da duniya.

Shugaban INEC bai rasu ba
INEC ta musanta labarin rasuwar Farfesa Mahmood Yakubu Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

An yaɗa labarin rasuwar Mahmood Yakubu

Jaridar TheCable ta ce wani rahoto a ranar Asabar ya yi iƙirarin cewa Mahmood Yakubu ya rasu ne a birnin Landan sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na rahoton na cewa:

Kara karanta wannan

"Ina jin zafi": Tinubu ya fadi abin da ya yi wa 'yan Najeriya ba da son rai ba

"Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ya rasu a birnin Landan bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Majiyoyi sun bayyana cewa ya kwanta cikin ƙoshin lafiya amma ya farka da matsanancin rashin lafiya."
"Duk da ƙoƙarin da iyalansa suka yi na samar masa kyakkyawar kulawa ta hanyar kai shi Landan domin jinya, an ce ya mutu."

INEC ta musanta labarin rasuwar shugabanta

Sai dai da yake magana a shafin X na INEC, babban sakataren yaɗa labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya yi watsi da rahoton a matsayin labarin ƙarya.

Rotimi Oyekanmi ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su yi watsi da labarin.

"Rahoton labarin ƙarya ne. Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wannan labari ke yaɗuwa ba. Tun a ranar Asabar din da ta gabata suka fara yaɗa shi."
"Ba zato ba tsammani wani dandalin labarai ya fara ba da labarin. Shugaban INEC yana cikin ƙoshin lafiya."

- Rotimi Oyekanmi

Shugaban INEC ga magantu kan zaɓen Ghana

Kara karanta wannan

Ministan shari'a ya fadi shugabannin kananan hukumomin da za a garkame

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi tsokaci kan zaɓen shugaban ƙasar Ghana.

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana sha’awarsa kan yadda ƴan siyasar Ghana, ba sa sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya zuwa wata a lokacin zaɓe, saɓanin yadda ya zama ruwan dare a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng