'Ba Ku da Hankali ne': Akpabio ga Masu Fada da Ministan Tinubu, Ya Jero Dalilansa
- Sanata Godswill Akpabio ya kare ministan Abuja, Nyesom Wike kan yadda ake sukarsa saboda rushe-rushe a birnin
- Shugaban majalisar ya ce yana mamakin ya ga mutum yana fada da Wike saboda mai hankali ba zai yi fada da shi ba
- Hakan ya biyo bayan caccakar Wike da ake yi a Abuja musamman saboda yawan rusau da yake yi a birnin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan masu sukar Nyesom Wike.
Akpabio ya yabawa Ministan inda ya kwatanta shi a matsayin mutum mai son zaman lafiya.
Akpabio ya soki masu fada da Wike
Punch ta ruwaito cewa Akpabio ya fadi haka ne a taron karatun littafi da aka shirya don bikin zagayowar ranar haihuwar Wike a jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya ce babu wani mutum da ke da hankali da zai shiga rikici ko fada da ministan.
“Na yi magana da daya daga cikin abokaina, na ce masa ban ga dalilin da zai sa mutum ya yi fada da Wike ba."
"Idan ya yi ihu a wajen zama, kafin in isa bakin ƙofa ya manta, shi kansa zai ɗauki wayarsa ya kira ni, ya ce ‘yaushe za ka zo gida muyi abincin rana?"
"Kuma ya manta da muhawarar da muka yi, sai in ce masa, ‘bayan rigimar?, saboda ya manta."
- Godswill Akpabio
Maganganun Akpabio sun janyo dariya daga mahalarta taron saboda yadda ya san waye Wike, TheCable ta ruwaito.
Wike ya fadi abin da ke gabansa
A nasa bangaren, Wike ya ce ba ya damu da suka da ake masa kawai ya mayar da hankali wurin aiki.
“Gare ni, abin da ya fi muhimmanci a rayuwa shi ne, idan ka san abin da kake son yi, kuma ka san yadda kake son yi, to ka ci gaba."
"Abu daya da zan tabbatar wa da ku duka shi ne, za mu ci gaba da saka ku alfahari.
- Nyesom Wike
Hadimin Akpabio ya jawowa mai gidansa zagi
A baya, kun ji cewa an yi ta sukar Sanata Godswill Akpabio bayan hadiminsa ya yi katobara game da mutuwar matar gwamna.
Hadimin mai suna Uduak Udo ya nemi yafiyar Gwamna Umo Eno kan kuskuren taya shi murnar mutuwar matarsa.
Asali: Legit.ng