Manyan Malaman Izala da Darika Sun Samu Mukaman Gwamnati

Manyan Malaman Izala da Darika Sun Samu Mukaman Gwamnati

  • Gwamna Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya kaddamar da kwamitin Shura mai dauke da manyan malaman addini
  • Kwamitin zai ba da shawara kan al’amuran addinin Islama tare da taimakawa wajen tabbatar da adalci, mutunci, da zaman lafiya
  • Shugaban Kwamitin shi ne babban limamin Bida kuma shugaban kungiyar limaman jihar Neja, Sheikh Adamu Yakatun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kaddamar da kwamitin Shura wanda zai zama wata cibiya ta bayar da shawara a kan al’amuran addinin Islama.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a zauren majalisar Gidan Gwamnati da ke Minna, inda aka zabi mambobin kwamitin bisa cancantar su da rawar da suke takawa ga al’umma.

Malaman Neja
Gwamnan Neja ya kafa kwamitin shura. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka nada kwamitin ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Bago, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da korar na Kano, wani sakataren gwamnatin jiha ya ajiye aikinsa a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago ya yi kira ga mambobin kwamitin da su tabbatar da suna aiki da tsoron Allah tare da bin ka’idojin aikin da aka gindaya musu.

Manufar kafa kwamitin shura a Neja

Gwamna Bago ya bayyana cewa kwamitin na da nauyin bayar da shawarwari na addini ga gwamnan da kuma gwamnatin jihar kan duk wasu al’amuran da suka shafi addinin Islama.

Kwamitin zai yi aiki domin tabbatar da adalci da hadin kai ta hanyar tattaunawa da shawara tare da ba da gudummawa wajen samun zaman lafiya mai dorewa a jihar Neja.

Haka zalika, kwamitin zai taimaka wajen magance matsalolin rikice-rikicen addini ta hanyar bayar da shawarwari masu nagarta daga hukumar addini ta jihar Neja.

Shugabannin kwamitin shura a Neja

Babban limamin Bida, Sheikh Adamu Yakatun, shi ne shugaban kwamitin, yayin da Dr Umar Farooq Abdullahi daga hukumar addini ta jihar Neja zai kasance sakataren kwamitin.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno kai a tsakanin gwamnonin jihohi 36 kan kudirin harajin Tinubu

Sauran mambobin sun hada da limamai daga manyan masallatai da wakilai daga kungiyoyin addini irin su Tijjaniyya, JIBWIS, da FOMWAN.

'Yan kwamitin shura a jihar Neja

1. Shugaban kwamiti

Sheikh Alhaji Adamu Yakatun - Babban Limamin Bida

2. Sakataren Kwamiti

Dr Umar Farooq Abdullahi - Darakta-Janar, hukumar addini ta jihar Neja.

Sauran 'yan kwamitin shura a Neja

3. Sheikh Muhammad Ilyasu Abdulmalik - Babban Limamin Kontagora.

4. Malam Muhammad Shehu - Babban Limamin Borgu.

5. Sheikh Muhammad Kudu - Babban Limamin Agaie.

6. Malam Ridwan Nasir - Babban Limamin Suleja.

7. Malam Hassan Baba - Babban Limamin Lapai.

8. Malam Isah Jibrin Imam - Babban Limamin Minna.

9. Malam Umar Aliyu - Babban Limamin Kagara.

10. Dr Sulaiman Salahuddeen Omotosho - Wakilin CMS.

11. Malam Muhammad Usman - Wakilin Kungiyar Limamai.

Kara karanta wannan

Majalisar shura: Abba ya rabawa malaman musulunci kusan 50 mukamai a Kano

12. Malam Aliyu Adarawa - Wakilin JIBWIS Kaduna.

13. Malam Abubakar Abu Sumayya - Wakilin JIBWIS Jos.

14. Sheikh Muhammad Isah Kutigi - Wakilin Tijjaniyya.

15. Hajiya Aisha Abdulkareem Sambo - Wakiliya daga FOMWAN.

16. Hajiya Kulu Abdullahi - Wakiliya daga FOMWAN.

Abba ya ba malaman Kano mukami

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya sanar da nada 'yan majalisar Shura ta Kano mai kunshe da manyan malaman addini.

Legit ta wallafa cewa Farfesa Shehu Galadanci ne zai jagoranci majalisar, yayin da Shehu Wada Sagagi zai kasance sakataren majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng